Sport
Dollar
41,2910
0.2 %Euro
48,4340
0.61 %Gram Gold
4.758,6800
1.43 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Rahoton KCNA bai yi cikakken bayani kan sabbin makaman ba, sai dai kawai ya ce "makaman suna aiki ne da sabuwar fasaha ta musamman.
Shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, ya jagoranci gwajin harba sabbin makamai masu kare sararin samaniya guda biyu, kamar yadda kafar yada labarai ta gwamnati ta sanar a ranar Lahadi, bayan Pyongyang ta zargi Seoul da tayar da tarzoma a kan iyaka.
Gwajin harba makaman, wanda aka gudanar a ranar Asabar, ya nuna cewa sabbin tsarin makaman suna da "ƙwarewar yaki mai inganci," in ji rahoton kamfanin dillancin labarai na Koriya (KCNA).
Rahoton KCNA bai yi cikakken bayani kan sabbin makaman ba, sai dai kawai ya ce "makaman suna aiki ne da sabuwar fasaha ta musamman." Har ila yau, ba a bayyana inda aka gudanar da gwajin ba.
"Gwajin ya tabbatar da cewa fasahar sabbin makaman guda biyu tsaf za su kakkaɓo duk wasu hare-hare ta sama," in ji KCNA.
Comments
No comments Yet
Comment