Turkiyya ta kafa ɗaya daga cibiyoyin bincike da haƙar ma'adanai na zamani, da suka haɗa da jiragen ruwa huɗu na haƙar ma'adanai a tsakiyar teku, da jirage biyu na bincike da kuma jiragen tallafi.
Turkiyya tana shirin fara aiki a ɗaya daga wuraren haƙar zinare na Nijar a shekara mai zuwa, kamar yadda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya sanar, yana mai ƙarawa da cewa ƙasar na bincike a wuraren haƙar zinare a ƙasashen waje.
“Ba tare bai wa duniya da muhalli abin da ya kamace su ba, tattalin arzikin duniya ba zai bunkasa ba, ba za a tabbatar da tsaro a harkar makamashi ba, sannan ba za a samar da tsaro da kwanciyar hankali ba a duniya,” a cewar Erdogan ranar Juma’a yayin da yake wani jawabi ga Taron Makamashi na Istanbul, wani taron rana daya da aka gudanar a birnin na Turkiyya.
Taron na Makamashi na Istanbul, wanda kamfanin makamashi na Anadolu ya shirya ƙarƙashin Ma’aikatar Makamashi da Ma’adanai ya mayar da hankali kan taken “Makoma Bai Ɗaya, Manufofi Bai Ɗaya,” ya tattaro shugabannin a harkar makamashi daga faɗin duniya don tunkarar ƙalubalen da ake fuskanta.
Edrodgan ya ce, da bututun iskar gas gudan bakawai, da cibiyoyin gas guda biyu dake kan jiragen ruwa, da kuma mashigu 15, Turkiyya na da damar zama ɗaya daga cibiyoyin hada-hadar makamashi ta duniya.
Turkiyya tana fatan zama ɗaya daga cikin ƙasashe uku dake kan gaba a nahiyar Turai wajen samar da makamashi da ba ya gurɓata muhalli, tare da zama ɗaya daga ƙasashe tara dake kan gana a duniya daga nan zuwa 2025, kamar yadda ya bayyana.
Yana bayyana cewa burin Turkiyya shi ne ta kai matsayin samar da megawat 20,000 daga makamashin nukiliya daga nan zuwa 2050, Erdogan ya ce “Da zarar ta fara aiki Cibiyar Makamashin Nukiliya ta Akkuyu za ta biya kaso 10% na lantarkin da ake buƙata a Turkiyya, kuma ta kare sakin hayaki mai gurbata muhalli da ya kai tan miliyan 35.”
Nasarorin makamashi
Da yake jaddada cewa a wannan makon ne aka shiga rana ta 1000 ta yakin Rasha-Ukraine, lamarin da ya tirsasa Turai sake nazarin samar da makamashinta, Erdogan ya yi karin haske kan hatsarin dogaro kan ƙasashen waje don samun makamashi.
Sakamakon daidaitacciyar alaƙa da Turkiyya ke da ita da dukkan ɓangarorin biyu da ke yaki, Turkiyya na daya daga kasashen da suka tsaya da kafarsu a lokacin da aka shiga mawuyacin hali saboda yakin, in ji Erdogan.
Turkiyya ta samar da kayan zamani da ke cikin mafiya kyau a duniya da ke nema da hakar albarkatun mai, da suka hada da jiragen ruwa hudu na hakar mai, jiragen binciken mai a teku biyu, da jiragen da ke kawo agaji, Daraktan Sadarwa na Turkiyya Fahrettin Altun ya rawaito Erdogan na fadin hakan.
Wadannan muhimman kayayyaki sun bayar da dama wajen gano matattarar albarkatun gas mafi girma a tarihin Turkiyya da aka samu a tekun Bahar Maliya shekaru hudu da suka gabata. Al’umar Turkiyya sun fara amfani da gas din da aka samu a karkashin teku da zurfin mita 4,000 a 2023, in ji Erdogan.
Karuwar yawan gas da ake fitarwa kullum
Erdogan ya kuma bayyana shirye-shiryen fadada fitar da gas din ta hanyar fara hakar wata rijiyar, wadda ake sa ran za ta kara yawan gas din da ake fitarwa kullum zuwa kubikmita miliyan 20 kowacce rana nan da 2026 – adadin da zai biya bukatar rabin gidajen Turkiyya.
Kokarin da Turkiyya ke yi ya tsallake iyakokinta. Jirgin ruwan neman albarkatun mai na Oruc Reis ya fara neman mai a cibiyoyi uku a gabar tekun Somalia, hakan na bayyana burin kasar kan ayyukan makamashi a duniya.
Erdogan ya yi nuni ga rijiyar man fetur ta Gabar, daya daga cikin cibiyoyin man Turkiyya, inda Turkiyya ta samun man fetur mafi yawa.
A yanzu a kowacce rana ana fitar da sama da gangar danyen mai dubu 57,000, inda jimillar man cikin gida da na waje ya haura ganga dubu 155,000 a kullum. Tare da man da aka gano kwanan nan a Sirnak, Hakkari, da Van, Turkiyya na ci gaba da samun karin matattarar makamashin da za ta dinga fitarwa.