Ma’aikatar Harkokin Waje ta bukaci tsagaita wuta nan take

Turkiyya Ta Yi Gargadi Kan Faɗaɗar Rikici Tsakanin Isra’ila, Amurka da Iran

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta bayyana damuwa kan rikicin da ya ɓarke bayan hare-haren da Isra’ila da Amurka suka kai wa Iran, inda ta ce lamarin na barazana ga tsaron yankin da ma duniya baki ɗaya.

A wata sanarwa da ta fitar, ma’aikatar ta yi kira ga dukkan ɓangarorin da su tsagaita wuta nan take, tana mai nuna damuwa kan duk wani mataki da zai karya dokokin ƙasa da ƙasa ko ya jefa rayukan fararen-hula cikin haɗari. Ta kuma yi tir da duk wani mataki da zai iya ƙara ta’azzara rikicin.

Sanarwar ta jaddada cewa ya kamata a magance matsalolin yankin ta hanyar zaman lafiya, tare da bayyana shirye-shiryen Turkiyya na bayar da goyon baya ga tattaunawar sulhu, yayin da ta ce kare lafiyar ‘yan ƙasarta a yankunan da lamarin ke faruwa shi ne babban fifiko.

A wani yunƙurin diflomasiyya, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna ta wayar tarho da takwarorinsa da suka haɗa da Abbas Araghchi, Fuad Hussein, Badr Abdelatty da Sugiono, inda suka tattauna halin da ake ciki da matakan rage tashin hankali.

Tushen labari: TRT Hausa

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#