Sport
A wata tattaunawa da jaridar Financial Times, Fidan ya yi nuni da fata nagari mai cike da taka tsan-tsan game da dawowar tattaunawar Amurka da Iran, inda ya bukaci dukkan bangarorin da su mayar da hankali ga nukiliya, su kawar da afkuwar wani yakin.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya ce Amurka da Iran suna nuna alamun sassauci a kokarin farfado da yarjejeniyar nukiliya, amma ya yi gargadin cewa faɗaɗa batutuwan tattaunawar na iya tura yankin zuwa ga sabon rikici.
A wata hira da Jaridar Financial Times ta buga a ranar Alhamis, Fidan ya ce Washington ta nuna sha'awar sassauta bukatarta da ta daɗe tana kira ga Iran kan ta kawo ƙarshen duk wani sinadarin uranium - wani muhimmin batu a tattaunawar da ta gabata.
"Yana da kyau cewa Amurkawa sun bayyana a shirye suke su amince da sarrafa uranium da Iran ke yi amma bisa iyakancewa da tsari,," in ji Fidan ga jaridar.
Iran, wacce ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Hana Yaɗuwar Makamashin Nukiliya, ta ci gaba da nanata cewa habaka sinadarin 'yancinta ne na ikon mallaka.
Fidan ya ce Tehran ta bayyana a shirye take ta amince da iyakance yawan makamashin da za ta sarrafa, kamar yadda aka yi a yarjejeniyar nukiliya ta 2015.
"A yanzu Iraniyawa sun fahimci cewa suna bukatar cim ma yarjejeniya da Amurkawa, kuma Amurkawa sun fahimci cewa Iraniyawa suna da wasu iyakoki. Ba shi da amfani a yi kokarin tilasta musu," in ji shi.
‘Faɗaɗa tattaunawar na iya jefa yarjejeniyar cikin hatsari’
Duk da haka, Fidan ya yi gargaɗi mai ƙarfi game da faɗaɗa tattaunawa don magance shirin makami mai linzami na Iran da kuma goyon bayan da take bai wa ƙungiyoyin da ke da makamai a yankin.
"Idan Amurka ta dage kan magance dukkan batutuwan a lokaci guda... Ina jin tsoron ko da bayanan nukiliya ba zai ci gaba ba... sakamakon na iya zama wani yaƙi a yankin," in ji shi.
Tattaunawa kai tsaye tsakanin wakilan Amurka da jami'an Iran ta sake dawowa a Muscat a makon da ya gabata, wannan shi ne karo na farko da Washington take tattaunawa tun bayan yaƙin kwanaki 12 da Isra'ila ta yi da Iran a watan Yuni.
Duk ɓangarorin biyu sun bayyana taron a matsayin mai fa’ida, kuma sun nuna cewa ana sa ran yin ƙarin wani zaman.
Yayin da tsoaffin buƙatun Amurka suka haɗa da rage yawan makaman nukiliya na Iran da goyon bayan ƙungiyoyi kamar Hezbollah da Houthi, Shugaba Donald Trump kwanan nan ya ba da shawarar cewa yarjejeniyar nukiliya kawai za ta iya zama "abin karɓa."
Fidan ya ce ƙasashen yankin, ciki har da Turkiyya, suna aiki kan "ra'ayoyi masu amfani" don magance matsalolin tsaro ba tare da rushe batun nukiliya ba.
Ya jaddada cewa sake gina aminci tsakanin Iran da maƙwabtanta zai zama mai muhimmanci ga kowace yarjejeniya mai ɗorewa.
"Akwai gibin amincewa da ƙasashen yankin, kuma magance wannan batu yana da matuƙar muhimmanci," in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment