Dollar

40,7015

0.02 %

Euro

47,2204

1.43 %

Gram Gold

4.394,9300

2.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Ministan Makamashi na Turkiyya Alparslan Bayraktar ya bayyana cewa ana sa ran Turkiyya za ta rinƙa fitar da kimanin cubic meter biliyan biyu ta gas zuwa Syria, inda ake sa ran wannan gas ɗin zai samar da wutar lantarki ga gidaje miliyan biyar.

Turkiyya ta fara shigar da iskar gas cikin Syria

Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar ya bayyana cewa an fara jigilar iskar gas daga Turkiyya zuwa Syria.

Ya bayyana haka ne a yayin bikin buɗe bututun iskar gas na Turkiyya zuwa Syria a ranar Asabar, inda Bayraktar ya ce iskar gas daga Azerbaijan za ta rika shiga Syria ta hanyar Kilis, wani birni da ke kan iyakar Turkiyya da arewacin Syria.

An kammala haɗa bututun iskar gas daga Kilis zuwa Aleppo na Syria a ranar 21 ga Mayu, bayan gyaran bututun da ya lalace.

Ya bayyana cewa za a iya fitar da iskar gas har zuwa cubic meter biliyan 2 (BCM) a kowace shekara zuwa Syria, wanda zai samar da wutar lantarki ga gidaje miliyan 5.

Bayraktar ya kuma ce ana fitar da wutar lantarki zuwa Syria ta wurare guda takwas a halin yanzu, kuma ana sa ran ƙarfin zai ƙaru da kashi 25 cikin ɗari a farko, sannan ya ninka fiye da haka.

Tsarin samar da makamashi na Syria ya jigata matuƙa sakamakon yaƙin basasar da ya fara a shekarar 2011.

Wuraren samar da wutar lantarki, layukan watsawa, da tsarin iskar gas sun lalace sosai, wanda ya rage yawan wutar lantarki da ake samu a wasu yankuna zuwa awanni 3-4 kawai a kowace rana.

Bayan rugujewar gwamnatin Baath a watan Disamba na shekarar 2024, an fara aiki na wucin gadi a Syria, inda aka sanya gyaran tsarin samar da makamashi a matsayin mafi fifiko.

Turkiyya ta yi amfani da ƙwarewar fasaha da kusancinta da yankin, inda ta fara bayar da gudunmawa wajen sake gina tsarin makamashi a wannan lokaci.

A baya, Turkiyya ta taɓa samar da ƙaramin adadin wutar lantarki zuwa arewacin Syria, inda takan bayar da tallafi ta hanyar layukan watsawa a wasu lokuta.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#