An ware kuɗin ne domin inganta ayyukan rigakafi da shirin ko-ta-kwana da gano cututtuka masu yaɗuwa da wuri da kuma ɗaukar matakan gaggawa a faɗin ƙasar, in ji shugaban hukumar NCDC
Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce asusun gaggawa na naira biliyan 10 da gwamnatin tarayya ta ware, an yi shi ne domin ƙarfafa shirin tunkarar barazanar cututtuka masu yaduwa daban-daban, ba wai cutar Ebola kaɗai ba.
Darakta-Janar na hukumar, Dakta Jide Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin da yake mayar da martani kan ce-ce-ku-cen da ya bullo game da batun asusun, wanda gwamnatin tarayya ta amince da shi a watan Yunin 2026 bayan ɓarkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC).
Idris ya ce an ware kuɗin ne domin inganta ayyukan rigakafi da shirin ko-ta-kwana da gano cututtuka masu yaɗuwa da wuri da kuma ɗaukar matakan gaggawa a faɗin ƙasar.
Ya bayyana cututtukan Ebola da zazzaɓin lassa da kwalara da sankarau da mashako da ƙyanda da Mpox da kuma bijirewar ƙwayoyin cuta ga magungunan kashe su a matsayin wasu daga cikin barazanar lafiya da asusun zai taimaka wajen tunkara.
Kazalika ya bayyana cewa an miƙa kuɗin kai tsaye ga hukumar NCDC ne, ba ga Kwamitin Shugaban Ƙasa kan Cutar Ebola ba, wanda Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ke jagoranta.
A cewarsa, an kafa kwamitin ne musamman domin sa ido da kuma lura da ayyukan da Nijeriya ke yi na tunkarar cutar Ebola.
Idris ya buƙaci ’yan siyasa da sauran masu sharhi da su guji yaɗa bayanan ƙarya game da asusun, yana mai gargaɗin cewa yaɗa bayanan da ba daidai ba a lokacin da ake fuskantar barazanar lafiya na iya rage amincewa da yardar jama’a tare da kawo cikas ga matakan da hukumomi ke ɗaukawa kan yaki da cututtuka masu yaɗuwa.
Kuɗin bai kai buƙatun lafiyar jama’ar Nijeriya ba
Haka kuma Shugaban na NCDC ya ce naira biliyan 10 da aka ware ya yi kaɗan idan aka kwatanta da yawan kuɗaɗen da ake buƙata domin kare ƙasar daga barazanar annobar cututtuka.
Ya bayyana cewa aiwatar da Shirin Ayyukan Ƙasa kan Tsaron Lafiyar Jama’a na (NAPHS 2.0), wanda ya soma daga 2025 zuwa 2029, zai laƙume kimanin naira biliyan 522.
Hakan na nufin ana buƙatar kusan naira biliyan 104.4 a duk shekara, inda ya ce asusun naira biliyan 10 ke wakiltar kusan kashi biyu cikin ɗari na kuɗin da ake buƙata a shekara.
Idris ya ce ana buƙatar ci-gaba da zuba jari daga gwamnatin tarayya da gwamnatocin jihohi da abokan hulɗar ci-gaba domin rage giɓin kuɗaɗen.
Kasafin kuɗin NCDC ya ƙaru zuwa naira biliyan 22
Ya kuma bayyana cewa kasafin kuɗin hukumar ya ƙaru daga naira biliyan 4 a shekarar 2024 zuwa biliyan 7 a 2025, yayin da kasafin kuɗin ƙasa na 2026 ya ware mata naira biliyan 22.
Gwamantin tarayya ta kuma amince da wani asusun tallafin gaggawa na naira biliyan 5 a shekarar 2025, kafin ta ƙara amincewa da ƙarin naira biliyan 10 a watan Yunin 2026.
A yayin da ya tabo batun ƙiyasin Hukumar Kula da Shirye-shiryen Tunkarar Annoba ta Duniya (Global Preparedness Monitoring Board), Idris ya ce ƙasashe na buƙatar tsakanin dala ɗaya zuwa biyu ga kowane mutum a shekara domin samar da wadataccen shirin tunkarar annoba.
A Nijeriya, wadda ke da kimanin mutane miliyan 240, hakan na nufin ana buƙatar tsakanin dala miliyan 240 zuwa miliyan 480 a kowace shekara.
Ya yi kira da a tabbatar da gaskiya da riƙon amana wajen sarrafa kuɗaɗen da ake warewa domin kare lafiyar jama’a, yana mai cewa rashin isasshen kuɗaɗen na iya sa ɓarkewar cututtuka ta rikiɗe zuwa babbar matsala, wadda ka iya mamaye cibiyoyin lafiya tare da haddasa asarar tattalin arziki.
Nijeriya ta ƙara tsaurara matakan sa ido kan Ebola
Nijeriya ta tabbatar da ɓullar cutar Ebola nau’in Bundibugyo a karon farko a ƙasar a ranar 20 ga Oktoba, 2026, bayan da wata mata mai shekaru 42 ta shigo kasar ta Abuja daga Uganda dauke da cutar.
Bayan tabbatar da cutar, hukumomin lafiya sun ƙaddamar da aikin gano waɗanda suka yi mu'amala da mara lafiyar, da sa ido kan yaɗuwar cutar, da killacewa da kuma lura da lafiyar waɗanda ke cikin haɗari.
An tura lafiyar zuwa Swizerland tare da mijinta a ranar 26 aga Oktoba, bayan da yanayin lafiyarta ya inganta.
NCDC ta ce ta gano mutum 62 da suka yi hulɗa da ita, waɗanda ake ci gaba da sanya ido a kansu, inda ake sa ran kammala wa'adin sa-idon a ranar 13 ga Nuwamba.
Idris ya jaddada cewa zuba jari a fannin tsaron lafiyar jama’a yana da muhimmaci wajen kare rayuka da kuma hana ɓarkewar cututtuka har su rikiɗe zuwa manyan matsalolin ƙasa.
TRT Afrika — TRT Afrika
Hoto: Reuters

