Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Jirgin Farko Ya Sauka Bayan Kusan Shekaru Biyu Da Tsayawar Aiki

Sudan Ta Fara Sake Jigilar Matafiya Zuwa Filin Jirgin Khartoum

Sudan ta fara jigilar matafiya a cikin ƙasar zuwa filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Khartoum a karon farko tun bayan barkewar yaƙi tsakanin sojin Sudan da rundunar RSF a watan Afrilun 2023, inda wani jirgin kamfanin jiragen sama ya iso daga Port Sudan, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar ta ruwaito. TRT Hausa

Jirgin, na kamfanin jiragen saman Sudan, ya sauka a filin jiragen saman Khartoum ɗauke da matafiya fararen-hula, bayan kusan shekaru biyu da dakatar da aiki sakamakon yaƙin da ke gudana tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF, a cewar kamfanin dillancin labaran Sudan SUNA. TRT Hausa

Kamfanin jiragen saman Sudan ya bayyana cewa jigilar na nuna jajircewarsa wajen tallafa wa sufurin sama, sake haɗa biranen ƙasar da kuma sauƙaƙa wahalhalun tafiye-tafiye da ‘yan Sudan ke fuskanta tun bayan barkewar yaƙin. TRT Hausa

Kamfanin dillancin labaran SUNA ya bayyana matakin a matsayin muhimmin ci-gaba na dawo da jigilar matafiya zuwa filin jiragen saman Khartoum, tare da nuni da fara dawowar zaman lafiya da kuma komawar rayuwa a babban birnin ƙasar a hankali. TRT Hausa

A watan Oktoban da ya gabata, hukumar kula da sufurin jiragen sama na fararen-hula a Sudan ta sanar da shirin sake buɗe filin jirgin, sai dai an kai hare-hare ta jirage marasa matuƙa, inda sojin Sudan suka ce sun tare jiragen RSF da aka turo filin. TRT Hausa

Rufe filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Khartoum — babbar cibiyar sufurin sama ta Sudan — ya katse jigilar matafiya a faɗin ƙasar na tsawon lokaci, sakamakon matsayinsa na tsakiyar ƙasa da muhimmancinsa ga harkokin zirga-zirga. TRT Hausa


 

 
 
 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#