Spain ta ce Amurka da Isra’ila ba za su iya su kaɗai tsara tsarin duniya ba, tare da sukar yakin Iran.
Ministar tsaron Spain, Margarita Robles, ta bayyana cewa Amurka da Isra’ila ba su da ikon su kaɗai su tsara dokokin tsarin duniya, tana sukar abin da ta kira matakin da aka ɗauka ba tare da tuntubar ƙasashen duniya ba. Ta ce ba za a amince da yanayin da ƙasashe biyu za su iya ja duniya cikin yaƙi ba, tana mai bayyana rikicin Iran a matsayin wanda ya saba wa dokokin ƙasa da ƙasa.
Ta kuma bayyana cewa Spain ta ɗauki wasu matakai masu muhimmanci, ciki har da hana amfani da sansanonin sojan Amurka a Rota da Morón da kuma sararin samaniyarta wajen gudanar da duk wani aiki da ya shafi Iran. Ta kara da cewa Amurka ta nemi izinin amfani da wasu wuraren soji a Spain domin kai hari kan Iran, amma ba ta fayyace cikakkun bayanai ba.
Robles ta nuna damuwa cewa babu wanda ya san ainihin manufar wannan yaƙi, ko na siyasa ne ko tattalin arziki ko wani abu daban, tana gargadin cewa rikicin na iya tsawaita kuma ya zama mai hatsari. Duk da haka, ta jaddada cewa wannan matsayi ba yana nufin Spain za ta janye daga kawancen NATO ba ko kuma ta sauya dangantakarta da Amurka.
A baya-bayan nan, Shugaban Amurka Donald Trump ya yi barazanar dakatar da hulɗar kasuwanci da Spain saboda rashin goyon bayan harin Iran, amma gwamnatin Spain ta ce wannan bai shafi kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu ba.
Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB