Dollar

39,0314

0.28 %

Euro

44,3544

0.69 %

Gram Gold

4.216,7400

2.27 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan ta’addar Boko Haram ɗin suka yi ƙoƙarin kutsawa garin don kai hari.

Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 16 a Damboa na jihar Borno

Rundunar sojin Nijeriya ta ce ta yi nasarar kashe ‘yan Boko Haram 16 a garin Damboa na jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya.

A wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na X, ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da ‘yan ta’addar Boko Haram ɗin suka yi ƙoƙarin kutsawa garin don kai hari.

“Da misalin ƙarfe ɗaya na tsakar daren yau 23 ga watan Mayun 2025, gwarazan dakarunmu na rundunar Operation Hadin Kai suka hango ‘yan ta’addar ISWAP/BokoHaram a Damboa kuma ba tare da ɓata lokaci ba suka buɗe musu wuta,” in ji sanarwar.

Rundunar sojin ta ƙara da cewa ‘yan ta’addar sun yi nufin kai harin ne kan rundunar, amma gaggawar aika sojojin sama da na ƙasa ya sa aka yi nasara a kansu.

“Bayan shafe kusan awa biyu ana ba-ta-kashi, daga baya an yi nasarar tilasta wa ‘yan ta’addar miƙa wuya bayan da suka kwashi kashinsu a hannu.”

Rundunar ta ce dakarun sun yi nasarar kawar da ‘yan ta’adda 16 a ba-ta-kashin sannan kuma tana ci gaba da bibiyar yadda lamarin ya faru.

Sai dai ta ce lamarin ya shafi wani wajen ajiyar makamai a yayin ba-ta-kashin, amma tuni aka shawo kan abin ba tare da jawo wata illa ba.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#