Dollar

39,1011

0.04 %

Euro

44,4609

0.52 %

Gram Gold

4.202,2600

1.92 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Mallam Nuhu ya ce ta hanyar haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka yi, an daƙile ta’asar da ake yawan aikatawa waɗanda suka haɗa da kashe-kashen jama’a da lalata wurare da sace-sacen jama’a da kuma hare-haren ta’addanci a kan cibiyoyin gwamnati.

Gwamnatin Tinubu ta samu nasara kan matsalolin tsaron da ta gada daga gwamnatin baya – Ribadu

Babban Mai Bai Wa Shugaban Nijeriya Shawara Kan Harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, ya ce gwamnatin tarayya da jami’an tsaro a ƙasar sun ci ƙarfin matsalolin tsaro da dama da gwamnatin Bola Tinubu ta gada.

Mallam Nuhu ya ce ta hanyar haɗin gwiwa da jami’an tsaro suka yi, an daƙile ta’asar da ake yawan aikatawa waɗanda suka haɗa da kashe-kashen jama’a da lalata wurare da sace-sacen jama’a da kuma hare-haren ta’addanci a kan cibiyoyin gwamnati.

Ribadu ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a wajen taron jam’iyyar APC domin murnar cika shekara biyu da hawan Shugaba Tinubu kan mulki.

Ribadun ya bayyana cewa Tinubu ya gaji manyan matsaloli biyar a faɗin ƙasar.

Ya bayyana cewa a baya, ‘yan ta’adda suna cin karensu ba babbaka a ƙasar inda ‘yan ƙasar ke fuskantar hare-hare a hanyar Abuja zuwa Kaduna, da gidan fursunan Kuje da wani harin da aka kai wata coci a Owo da wanda aka kai wata bataliyar soji a Bwari da ke Abuja.

Ya lissafo matsalolin tsaro da gwamnatin Tinubu ta gada waɗanda suka haɗa da na Boko Haram a arewa maso gabas da ‘yan fashin daji a arewa maso yamma da ‘yan awaren IPOB/ESN a kudu maso gabashin Nijeriya da yankin Neja Delta, da rikicin manoma da makiyaya a arewa maso tsakiyar Nijeriya.

Ribadu ya ƙara da cewa an kashe ‘yan Boko Haram fiye da 13,543 a cikin shekara biyu sannan an ƙwato makamai fiye da 11,000 da kuma lalata su a hannun ‘yan ta’adda.

Haka kuma Ribadu ya ce akwai ‘yan Boko Haram fiye da 124,408 da iyalansu da suka yi saranda tun bayan hawan gwamnatin Tinubu.

 

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#