Dollar

39,1011

0.04 %

Euro

44,4609

0.52 %

Gram Gold

4.202,2600

1.92 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

‘Muna kare gida da Jamhuriyya kuma muna ɗaukar mataki don bunƙasawa da ɗaga darajar Turkiyya, abin da zai dauwama har abada, a kowane ɓangare', a cewar Recep Tayyip Erdogan.

Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi bikin Ranar Ataturk da ta Matsa da Wasanni

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi bikin tunawa da ranar Ataturk, da ta Matasa da Wasanni.

A saƙon da ya tura ta hanyar Hukumar Sadarwa ta Turkiyya a shafin X ranar Litinin, Erdogan ya jaddada muhimmancin tarihi na ranar 19 ga Mayu, wadda ta zama ranar farko ta Yaƙin 'Yancin Kai na Turkiyya wanda Mustafa Kemal Ataturk, da ya kafa Jamhuriyar Turkiyya, ya jagoranta a shekarar 1919.

"Muna kare ƙasa da Jamhuriya—amanar da magabatanmu suka bar mana—kuma muna ɗaukar matakai don ci gaba da ɗaukaka Jamhuriyar Turkiyya, wadda za ta dawwama har abada, a kowane fanni," in ji shugaban Turkiyya.

Erdogan ya jaddada cewa yana kallon matasan Turkiyya ba kawai a matsayin masu tsara makoma ba, amma kuma a matsayin ƙarfafa sauyi, inda ya ce yana da cikakken imani cewa tare da kuzari, da jajircewa, da mafarkinsu—tare da riƙe amanar al'adunmu a zukatansu—matasan Turkiyya za su bar wani babban tarihi "a zamaninmu a matsayin 'Ƙarni na Türkiye.'"

Makomar Turkiyya

Dangane da gina makomar Turkiyya, "muna warwarewa kuma muna kawar da kowace matsala da za ta ɓata kuzarin matasanmu da albarkatun ƙasar da "tattaunawa mara fa’ida," in ji shi.

"Muna aiki da duk ƙarfinmu don cika alkawarinmu na bar wa matasanmu ƙasa mai zaman lafiya da kwanciyar hankali, da fasahar zamani, da wadata."

"Muna bayar da damar da matasanmu za su gano basirarsu a kowane fanni, daga kimiyya zuwa fasaha, wasanni zuwa noma, diflomasiyya zuwa fasahar nukiliya, kuma muna tafiya tare da matasanmu don cim ma burinmu na Turkiyya mai girma da ƙarfi," in ji shugaban.

Ya ce za su ci gaba da tallafa wa duk matasan Turkiyya waɗanda ke aiki tukuru don cim ma burinsu, ba su taɓa yin ƙasa a gwiwa ba, kuma suna son ƙara ɗaukaka gadon al'adu da suka gada daga kakanninsu.

Ranar Matasa da Wasanni

Shugaban Turkiyya ya bayyana cewa za su ci gaba da nuna ƙuduri na yin aiki tuƙuru da cim ma nasarori masu yawa don matasan Turkiyya ta hanyar yaba musu a kowace nasara da Turkiyya ta samu, "wadda ta zama ƙasa mai muhimmanci yayin da take ƙara ƙarfi kuma ta ƙarfafa matsayinta da matakan da muka ɗauka."

Erdogan ya kuma yi jinjina wa "duk jaruman Yaƙin 'Yancin Kai namu, musamman Gazi Mustafa Kemal."

Ranar 19 ga Mayu, 1919, ita ce ranar da Ataturk, wanda daga baya ya kafa Jamhuriyar Turkiyya, ya isa birnin Samsun na bakin teku daga Istanbul don ƙaddamar da yaƙin da bayan shekaru huɗu ya sauya ƙasar zuwa Turkiyya ta zamani.

A shekarar 1938, Ataturk ya keɓe ranar 19 ga Mayu ga matasan ƙasar Turkiyya a matsayin Ranar Matasa da Wasanni, wata rana ta ƙasa wadda matasa ke shiga cikin ayyukan wasanni da al'adu tare da bukukuwan hukuma a fadin ƙasar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#