Sport
Dollar
39,1011
0.04 %Euro
44,4609
0.52 %Gram Gold
4.202,2600
1.92 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ana sa ran wannan ziyarar za ta ƙara yauƙaƙa dangantaka tsakanin ƙasashen biyu a muhimman ɓangarori waɗanda suka haɗa da kasuwanci da makamashi da yawon buɗe ido.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, zai kai ziyara zuwa Tarayyar Rasha a ranakun 26 zuwa 27 ga Mayu, 2025, bisa gayyatar gayyatara da takwaransa Sergey Lavrov ya yi masa a hukumance.
A lokacin wannan ziyara, ana sa ran Fidan zai gana da Shugaban Rasha, Vladimir Putin, tare da gudanar da tattaunawa a hukumance da Lavrov a birnin Moscow, kamar yadda majiyoyin Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya suka bayyana a ranar Asabar.
Ziyarar za ta mayar da hankali kan muhimman fannoni na dangantakar Turkiyya da Rasha, inda ake sa ran Fidan zai yi cikakken nazari kan haɗin gwiwar kasashen biyu a fannonin kasuwanci, makamashi, da yawon shakatawa.
Haka kuma, za a tattauna matakan da za a ɗauka don yauƙaƙa dangantakar ƙasashen biyu.
Baya ga ganawarsa da Lavrov da Putin, Fidan zai kuma tattaunawa da wasu manyan jami’an gwamnatin Rasha.
Jami’an haɗa da Mataimakin Shugaban Ma’aikatar Shugaban Kasa, Vladimir Medinsky, wanda ya jagoranci tawagar Rasha a tattaunawar Rasha da Ukraine da aka gudanar a Istanbul a ranar 16 ga Mayu, da kuma Ministan Tsaro, Andrei Belousov, da wasu manyan jami’ai.
Tattaunawar za ta kuma ƙunshi batutuwan da suka shafi ƙarin haɗin kai tsakanin ƙasashen biyu.
Ana sa ran a yayin tattaunawar Fidan zai ƙara jaddada ƙoƙarin da Turkiyya ke yi wajen samar da zaman lafiya mai ɗorewa da adalci a rikicin da ke tsakanin Rasha da Ukraine, tare da bayyana jin daɗinsa kan ci gaban da aka samu kwanan nan da zai iya taimakawa wajen samun nasara a wannan fanni.
Haka kuma, Fidan zai sake jaddada shirye-shiryen Turkiyya na ci gaba da taka rawa a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar gaba tsakanin ɓangarorin da ke rikici, kamar yadda ta yi a baya a shekarar 2022 da kuma a zagayen tattaunawar da aka yi a ranar 16 ga Mayu.
Ziyarar za ta kuma ƙunshi musayar ra’ayoyi kan batutuwan yankin da na kasa da kasa, ciki har da halin da ake ciki a Syria, Gaza, da yankin Kudancin Caucasus
Ziyarar da Fidan ya kai ta ƙarshe Rasha ya yi ta ne tsakanin 10 zuwa 11 ga Yunin, 2024, inda ya halarci taron BRICS+, sannan daga baya ya halarci taron Ƙolin BRICS a ranar 24 ga Oktobar 2024, tare da Shugaba Recep Tayyip Erdoğan.
Ganawa ta baya-bayan nan da Fidan da Lavrov suka yi sun yi ta ne a ranar 12 ga Afrilun 2025, a gefen taron Antalya Diplomacy Forum. Kafin wannan, Lavrov ya ziyarci Turkiyya a ranar 23 ga Fabrairun 2025, domin tattaunawar bangarorin biyu.
Haka kuma, ya halarci taron dandalin hadin kai na yankin 3+3 da Fidan ya shirya a Istanbul a ranar 18 ga Oktobar 2024. Bugu da kari, ministocin biyu sun yi ganawa ta ɓangarorin biyu a lokacin taron ministocin harkokin waje na G20 da aka gudanar a Johannesburg a ranar 20 ga Fabrairun 2025.
Comments
No comments Yet
Comment