Tokyo: 05:22 AM
Londra: 08:22 PM
New York: 03:22 PM
İstanbul: 11:22 PM

Dollar

39,5320

0.13 %

Euro

45,3900

-0.13 %

Gram Gold

4.279,8400

-0.49 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

An bayar da kambin ‘Golden Tower’ shirin bin kwakkwafi na TRT World mai suna “Holy Redemption”.

TRT World ta lashe Kambi Hudu a Bikin Kyaututtuka na Fim da Talabijin na ‘2025 New York Festival’

An ba wa TRT World manyan kambi hudu, a wajen bikin bayar da Kyaututtuka na Fim da Talabijin na New York 2025.

TRT World da ta shiga takarar neman kambin kafafen yada labarai na duniya, ta lashe kambi a bangarori daga binciken kwakkwafi a aikin jarida zuwa alakar kasa da kasa, al’amuran yau da kullum zuwa da tallace-tallace da sauransu.

An bayar da kambin ‘Golden Tower’ ga shirin bin kwakkwafi na TRT World mai suna “Holy Redemption”

Shirin fim din ya kuma lashe kambin ‘Silver Tower’ a bangaren alakar kasa da kasa.

A shirin ‘Holy Redemption’, na bayanin yadda ‘yan jaridar TRT World, suka lallaba da shiga cikin Yahudawa ‘yan kama guri zauna a Yammacin Kogin Jordan, tare da bankado yadda ake kwace kasa da gonakin Falasdinawa cikin tsari.

Shirin, ya yi aikin jarida na gaskiya wajen bayyana yadda ake take hakkokin dana dam na jama’ar yankin, da mummunan halin da fararen hula ke ciki, da yadda ake take dokokin kasa da kasa.

A bangaren shirin labarai, an baiwa shirin ‘Tallata Bikin Cikar TRT Shekaru 9 da Kafuwa” kambin ‘Silver Tower’.

Wannan shirin fim na talla, ya bayyana wa masu kallo cikin hotuna da bidiyo manufar yada shirye-shirye da manufofin tashar.

Kazalika, an bai wa fim din “Yemen: The Third Frontier” kambin ‘Silver Tower’ a bangaren wasu al’amura da suka afku.

Shirin ya yi duba kan irin halin da al’uma suka fada sakamakon yakin Yaman, inda ya nun wa duniya bangarorin yakin da ba ta taba gani ba.

Ma’aikatan TRT World, sun isa ga wajen da jirgin ruwa na farko mai suna ‘Galaxy Leader’ da aka kwace daga hannun mayakan Houthi, sun nuna asalin yadda yakin ke gudana da halin yunwa da rashin samun kula da lafiya da ake ciki, da karancin kayan taimako da sauran matsaloli da dama a Yaman.

Wannan nasara, na bayyana yadda TRT World ke ci gaba da taka rawa a fagen aikin jarida a duniya tare da nua kwarewar aiki da kara karfi a idanuwan jama’a.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#