Dollar

39,0309

0.28 %

Euro

44,3492

0.68 %

Gram Gold

4.217,5900

2.29 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A bikin iyali na ƙasa da ƙasa, Uwargidan Shugaban ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta yi kira ga duniya ta haɗa kai wajen kare kyawawan ɗabi’u da mutuncin iyali yayin da ake ƙara samun barazana ga ginshiƙan al’adu.

Emine Erdogan: 'Iyali shi ne tushen gina al’umma'

Emine Erdogan, Uwargidan Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ta gabatar da jawabi a wani bikin da aka yi a wani ɓangare na taron tattaunawa kan iyali na ƙasa da ƙasa, wanda ma’aikatar Iyali da Hidima ga Al’umma ta shirya.

Yayin da take nuna yadda taron ke ƙara samun farin jini, Emine Erdogan ta ce, "Na yi imanin cewa muna tarayya ne cikin damuwarmu. Dukkanmu a duniya ta yau inda barazana ga iyali ya ƙaru sosai, muna son mu kare hakan."

Ta bayyana imaninta cewa taron shi ne "mataki na farko na haɗin kai mai ƙarfi domin cim ma wannan manufa."

Muhimmin tushen gina al’umma

Yayin da take bayyana iyali "a matsayin mafi muhimmancin tushen gina al’umma," Uwargidan Shugaban Ƙasar ta jaddada rawar da yake takawa a matsayin tushen ɗabi’u masu kyau da tsaro da kuma abin da ke bambanta ƙasa da sauran ƙasashe.

Ta bayyana cewa, "Tamkar yadda muke dasa reshen fure cikin ruwa domin ya hayayyafa, iyali shi ne tushe inda cibiyoyin wayewar al’umma ke haɓaka."

Emine Erdogan ta yi gargaɗi game da “barazana ta duniya” da ke zazzage ginshiƙan iyali, tana mai cewa suna da niyyar “mamaye kariyar ne daga ciki” ta hanyar mayar da hankali kan zuƙatan yara.

Ta yi kira ga gwamnatoci su ƙara himma wajen samar da manufofi na kariya, tana mai cewa, "Iyali abu ne da al’ummomi a sassan duniya ke mutuntawa kuma wani abu ne mai tsarki a kowane addini."

Turkiyya ta ayyana 2025 a matsayin shekarar iyali

Da take ayyana shekarar 2025 a matsayin "Shekarar Iyali," Emine Erdogan ta bayyana shirye-shiryen Turkiyya wajen ƙarfafa haɗin kan iyali ciki har da aure da tallafin yara da shirye-shiryen reno da “Shirin Zuƙatun Sa kai”, wanda UNICEF ya yabawa.

Ta kuma yi bayani game da kyawawan dabi’un iyali na Turkiyya masu tarihi, tana mai cewa "al’adar Turkiyya tana bai wa ‘yan’uwa muhimmanci inda kakanni da jikoki da yawa ke zama tare."

Da take magana kan wani binciken Jami’ar Harvard, ta ƙara da cewa, "Sirrin jin daɗin ɗan’adam shi ne iya ƙulla alaƙa mai ƙarfi kuma mai ɗorewa da mutane da yawa.”

Da take tunani game da wahalar da ake sha a duniya, Emine Erdogan ta ce, "tun ranar 7 ga watan Oktoba na shekarar 2023, an shafe sama da iyalai 2,000 a Falasɗinu," tana mai kira ga ƙasashen duniya ka da su yi watsi da rikicin.

Jajircewa domin iyali da duniya

A matsayin wani ɓangare daga cikin shirin, wakilai daga ƙasashe 15 sun rattaba hannu  kan shelar kawar da shara ta duniya wadda aka ƙaddamar a zama babban zauren MDD na 78.

Ministoci da manyan jami’ai daga Falasdinu da Nijeriya da Senegal da Malaysia da Kyrgyzstan da sauransu su ma sun jaddada jajircewarsu kan lamarin.

Ministar iyali da hidima ga al’umma, Mahinur Ozdemir Goktas, ta miƙa wani zanen bishiyar iyali ga Emine Erdogan a bikin.

Daga baya, Emine Erdogan ta wallafa wani saƙo a shafukan sada zumunta  inda ta jaddada cewa, "Iyali shi ne kadarar bil’adama mafi daɗewa kuma mafi daraja … da wannan imanin, na yi murnar halartar bikin taron ƙasa da ƙasa kan iyali.” 

An fara taron ƙasa da ƙasa kan iyali ne a Istanbul ranar Alhamis inda ministoci daga ƙasashe 27 suka halarta.

Taron na kwanaki biyu, da ake yi a ƙarƙashin taken "Iyalinmu, Makomarmu," an shirya shi ne ƙarƙashin jagorancin Ma’aikatar Iyali da Hidima ga Al’umma  a wani ɓangare na shirin 2025 shekarar Iyali.

Ana sa ran Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai gabatar da jawabin rufe taro.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#