Sport
Dollar
39,1011
0.04 %Euro
44,4609
0.52 %Gram Gold
4.202,2600
1.92 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban Serbia Aleksandar Vucic ya ce ƙasarsa na mutunta dangantakarta da Turkiyya domin samun kwanciyar hankalin yankin yayin ganawarsa da Hakan Fidan.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da shugaban ƙasar Serbia Aleksandar Vucic a ranar Litinin a ziyarar da ya kai birnin Belgrade a cewar ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya.
Bayan ganawar, Vucic ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa, ya ji daɗin karɓar baƙuncin Fidan, ya kuma jaddada muhimmancin da Serbia take baiwa dangantakarta da Turkiyya domin samun zaman lafiya a yankin.
Vucic ya bayyana dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu bisa ga tataunawar siyasa mai karfi da kuma haɗin gwiwa a fannonin da suka hada da tattalin arziki, makamashi, yawon bude ido, al'adu da ilimi.
Ya yi marhabin da kuɗurin Turkiyya na halartar bikin baje kolin duniya na 2027 a Belgrade, yana mai cewa hakan wata alama ce ta haɗin gwiwa mai karfi da amincewa da juna tsakanin ƙasashen biyu.
"Serbiya tana ba da muhimmanci na musamman ga dangantakarta da Turkiyya, wanda ya kasance babban jigo a zaman lafiyar yankin," in ji Vucic.
Fidan ya kuma gana da ministan harkokin wajen Serbia Marko Djuric da wasu jiga-jigan siyasar Sabiyawa a ofishin jakadancin Turkiyya da ke babban birnin ƙasar.
Daga cikin wadanda suka halarta sun haɗa da Rasim Ljajic, da shugaban jam'iyyar Social Democratic Party; Usame Zukorlic, da shugaban jam'iyyar Justice da Reconciliation, da kuma ministan sulhu, da haɗin gwiwar yankin, da zaman lafiyar al'umma; da Ahmedin Skrijelj, ɗan majalisa mai wakiltar Jam'iyyar Democratic Action na Sandzak daga Novi Pazar.
Comments
No comments Yet
Comment