Dollar

39,1011

0.04 %

Euro

44,4609

0.52 %

Gram Gold

4.202,2600

1.92 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Erdogan ya karɓi baƙuncin al Sharaa a ranar Asabar inda aka gudanar da bikin tarbarsa a hukumance a Ofishin Shugaban Ƙasa na Dolmabahce da ke Istanbul.

Shugaban Turkiyya Erdogan ya tattauna da Shugaban Syria al Sharaa a Istanbul

Shugaban ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya gana da shugaban ƙasar Syria, Ahmad al Sharaa, a birnin Istanbul.

Erdogan ya karɓi baƙuncin al Sharaa a ranar Asabar inda aka gudanar da bikin tarbarsa a hukumance a Ofishin Shugaban Ƙasa na Dolmabahce da ke Istanbul.

Taron ya samu halartar Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan, Ministan Tsaron Ƙasa Yasar Guler, Shugaban Leƙen Asirin Turkiyya Ibrahim Kalin, Shugaban Ma'aikatar Masana'antar Tsaro ta Turkiyya Haluk Gorgun, Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad al Shaibani da wasu jami'ai da dama.

An gudanar da taron ne ƙofa a garƙame.

Tattaunawar ta zo ne bayan da Amurka da Tarayyar Turai suka fara ɗage takunkumin da suka ƙaƙaba wa Syria, kuma ziyarar da al Sharaa ya kai Turkiyya ita ce ta farko tun bayan ɗaukar matakin.

Shugaba Erdogan ya yi maraba da matakin, yana mai cewa, Turkiyya na kallon sassauta takunkumin ta fuska mai kyau. Ya jaddada muhimmancin kiyaye iyakokin kasar ta Syria da tabbatar da mulkin ƙasar a ƙarƙashin hukuma guda ɗaya.

Erdogan ya bayyana cewa yana da yaƙinin cewa Syria na tafiya a kan hanya mai kyau kuma tana kan hanyar samun zaman lafiya, inda ya kuma ƙara jaddada goyon bayan da Turkiyya ta jima tana bayarwa.

“Kamar yadda muke tare da Syria har zuwa yanzu, za mu ci gaba da yin haka,” kamar yadda ya bayyana a lokacin tattaunawar.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#