Dollar

40,6910

0.06 %

Euro

47,3116

0.04 %

Gram Gold

4.413,8600

0.07 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da lambobin yabo ga kowace ‘yar wasan tawagar Nijeriya ta ƙwallon kwando ta mata, wato D’Tigress.

Shugaban Nijeriya ya ba da kyautar dala $100,000 da lambar yabo ga 'yan wasan D’Tigress

Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana kyautar dala $100,000 da kuma lambar yabo ga duka ‘yan wasan tawagar mata ta ƙwallon kwando ta ƙasar, wato D’Tigress.

Sannan an bai wa kowane jami’an horar da ƙungiyar dala $50,000.

Tawagar ce ta lashe gasar ƙwallon kwando ta Afirka, ta 2025, wato FIBA AfroBasket, wanda shi ne karo na biyar a jere da ta samu wannan nasara.

Shugaban ya samu wakilcin mataimakinsa, Kashim Shettima a bikin tarbar ‘yan wasan da aka yi a fadar shugaban ƙasa ta Aso Rock da ke birnin Abuja ranar Litinin.

Tawagar ƙarƙashin kocin tawagar, Rena Wakama ta samu kyakkyawar tarba daga Kashim Shettima, tare da mai ɗakin shugaban ƙasa, Oluremi Tinubu, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila.

A ranar Lahadi ne ‘yan matan suka doke takwarorinsu na Mali da ci 78–64 a gasar da aka kammala a filin wasa na Palais des Sports de Treichville da ke birnin Abidjan na Ivory Coast.

A kwanakin da suka gabata ma Shugaba Tinubu ya yi makamancin wannan kyautar ga ƙungiyar mata ta ƙwallon ƙafa, ta Super Falcons wadda ta lashe kofin Afirka na WAFCON a birnin Rabat na Morocco.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#