Dollar

42,8964

0.1 %

Euro

51,1406

0.43 %

Gram Gold

6.207,9400

0.24 %

Quarter Gold

10.205,2300

0 %

Silver

98,9300

0.43 %

An ƙare rabin farko na wasan yayin da Zimbabwe take da ci 1-0 kan Zimbabwe, bayan da Marmoush ya farke, sannan Salah ya ci ta biyu a mintin ƙarshe.

Salah ya ci ƙwallo a mintin ƙarshe don bai wa Masar nasara kan Zimbabwe a AFCON

Mohamed Salah ya ƙwato nama a bakin kura a wani wasa da ya ƙayatar wanda sai a dab da ƙarshe Masar ta doke Zimbabwe da ci 2-1 a wasansu na farko na gasar Kofin Ƙasashen Afrika a Maroko.

Kyaftin ɗin Masar, Mohamed Salah ne ya ci ƙwallon a minti na 91, wanda ya ba su nasara a gasar da suka taɓa lashewa sau bakwai.

Zimbabwe ce ta fara cin ƙwallo a minti na 20 ta hannun Prince Dube a wasan da aka buga a maraicen Litinin.

Sai a minti na 64 ɗan wasan Masar, Omar Marmoush ya farke ƙwallon, kafin da a ƙarshe Salah ya kai su gaci.

A rukunin, ƙasashen Masar da Zimbabwe, Afirka ta Kudu ta yi nasara kan Angola da ci 2-1, wanda ke nufin Masar da Afirka ta Kudu suna saman teburi da maki uku kowannensu.

Masar dai ita ta fi kowace ƙasar Afirka zuwa gasar AFCON har sau 26, inda suka buga wasannin 111, suka ci ƙwallo 175, sannan suka ci kofi sau 7.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#