Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ivory Coast ta fitar da jerin 'yanwasan da za su buga mata Gasar AFCON 2025, inda Wilfried Zaha na Charlotte FC da Amad Diallo Manchester United suka samu kiranye, amma Nicolas Pepe na Villarreal ya rasa.
Kusan mako guda ne ya rage kafin buɗe gasar ƙwallon ƙafa ta ƙashashen Afirka, AFCON a Marocco. Ƙasashe 24 ne za su fafata don neman ɗaga kofin da ya fi kowanne a nahiyar.
Ɗaya-bayan-ɗaya ƙasashen suna ayyana jerin ‘yanwasan da za su wakilce su a gasar, inda a yanzu Ivory Coast ta fitar da sunayen tawagarta.
Sanarwar Ivory Coast ta nuna cewa Wilfried Zaha, ɗanwasan Charlotte FC ta Amurka, wanda ya shekara biyu ba tare da ya samu gayyata ba, yanzu ya samu shiga tawagar.
Sai matashin ɗanwasan Manchester United, Amad Diallo shi ma ya samu gayyatar zuwa gasar da za a fara ranar 21 ga Disamba.
Sai dai ɗanwasan Villarreal, Nicolas Pepe, wanda ya gaza samun tagomashi a Arsenal ya gaza samun goron gayyatar shiga tawagar Ivory Coast mai ɗauke da ‘yanwasa 26.
Komen Zaha
Mai shekaru 33, Wilfried Zaha ya yi taƙaddama da tsohon kocin ƙasarsa, Patrice Beaumelle, wanda ya yi sanadin hana shi shiga tawagar da ta lashe kofin AFCON na 2023 a gida.
Kocin tawagar ta The Elephants na yanzu, Emerse Fae shi ya zaɓi maido da Zaha cikin tawagar, kamar yadda ya faɗa ranar Talatan nan.
Zaha dai ya yi wasa a Crystal Palace ta Ingila, da Galatasaray ta Turkiyya, kafin ya koma Charlotte FC ta jihar Carolina a Amurka.
Wani ɗanwasan da shi ma ya gaza samun damar waklitar ƙasarsa shi ne Simon Adingra na Sunderland FC ta Ingila.
Mai shekaru 23, Adingra ya taimaki ƙasarsa wajen doke Nijeriya a wasan ƙarshe na gasar AFCON ta bara.
Jerin ‘yanwasa 26 na Ivory Coast
Masu tsaron gida: Yahia Fofana (Caykur Rizespor ta Turkiyya), Mohamed Kone (Charleroi ta Belgium), Alban Lafont (Panathinaikos ta Girka).
Masu tsaron baya: Emmanuel Agbadou (Wolves ta Ingila), Willy Boly (Nottingham Forest ta Ingila), Ousmane Diomande (Sporting ta Portugal), Guela Doue (Strasbourg ta Jamus), Ghislain Konan (Gil Vicente ta Portugal), Odilon Kossounou (Atalanta ta Italiya), Evan Ndicka (Roma ta Italiya), Christopher Operi (Istanbul Basaksehir ta Turkiyya), Armel Zohouri (Iberia 1999 ta Georgia).
‘Yanwasan tsakiya: Seko Fofana (Rennes ta Faransa), Jean-Philippe Gbamin (Metz ta Faransa), Christ Inao Oulai (Trabzonspor ta Turkiyya), Franck Kessie (Al-Ahli ta Saudiyya), Ibrahim Sangare (Nottingham Forest ta Ingila), Jean-Michael Seri (Maribor ta Slovenia).
‘Yanwasan gaba: Vakoun Bayo (Udinese ta Italiya), Oumar Diakite (Cercle Brugge ta Belgium), Amad Diallo (Manchester United ta Ingila), Yan Diomande (RB Leipzig ta Jamus), Sebastien Haller (Utrecht ta Netherlands), Jean-Philippe Krasso (Paris FC ta Faransa), Bazoumana Toure (Hoffenheim ta Jamus), Wilfried Zaha (Charlotte ta Amurka).
‘Yan ko-ta-ɓaci: Evann Guessand (Aston Villa ta Ingila), Guiagon Parfait (Royal Charleroi ta Belgium).
Comments
No comments Yet
Comment