Sport
Dollar
42,5354
0.07 %Euro
49,5729
-0.06 %Gram Gold
5.744,6300
-0.15 %Quarter Gold
9.538,1500
0.27 %Silver
79,8400
2.28 %Cristiano Ronaldo ya faɗaɗa kasuwancinsa ta hanyar zuba jari a kamfanin ƙirƙirarriyar basira na Perplexity wanda ke bin sahun ChatGPT.
Gwarzon ɗanƙwallon ƙafa ɗan asalin Portugal, Cristiano Ronaldo ya zuba jari a sanannen kamfanin ƙirƙirarriyar basira na Perplexity.
Shafin kamfanin shi ke biye wa shafin ChatGPT a farin jini, sakamakon yadda yake haɓaka har yake neman kamo ChatGPT.
Labarin zuba jarin da ɗanwasan da a yanzu yake taka leda a Al Nassr ta Saudiyya ya yi, ya zo ne cikin wata sanarwar bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta.
Wani ɓangare na jarin ya ƙunshi cewa Ronaldo zai zama jakadan kamfanin da aka kafa a 2022, da zummar inganta burin kamfanin na samun fifiko a faɗin duniya.
Wannan mataki na ɗanwasan mai shekaru 41 na nuni da yadda yake faɗaɗa dabarunsa na kasuwanci, wadda ya ƙunshi harkokin motsa-jiki, marabci, da ayyukan fasaha.
A halin yanzu, kamfanin Perplexity yana da kimar dala biliyan $20.
A baya-bayan nan, an ambato Ronaldo yana cewa ya yi amfani da shafin Perplexity don shirya jawabinsa, inda tun a lokacin aka yi tunanin suna da alaƙa.
Shafin na ƙirƙirarriyar basira ya yi suna wajen amsa tambayoyin masu amfani da shi, da kuma ƙirƙirar abubuwan da ake iya nunawa a allon kwamfuta ko waya.
Comments
No comments Yet
Comment