Dollar

42,5354

0.07 %

Euro

49,5729

-0.06 %

Gram Gold

5.744,6300

-0.15 %

Quarter Gold

9.538,1500

0.27 %

Silver

79,8400

2.28 %

Hukumar da ke yi wa Kamfanonin Rajista a Nijeriya ta yi gargaɗi game da masu gudanar da sana'ar POS ba tare da rajista ba inda ta ce daga Janairun 2026, jami'an tsaro za su fara rufe duk wani wurin sana’ar POS maras rajista.

Gwamnatin Nijeriya za ta fara rufe wuraren sana’ar POS marasa rajista daga Janairun 2026

Hukumar da ke yi wa Kamfanonin Rajista a Nijeriya (CAC) ta yi barazanar ɗaukar mataki kan masu gudanar da sana’ar POS waɗanda ba su yi rajista da ita ba daga 1 ga Janairun 2026.

Hukumar ta ce ta kula da yadda ake samun ƙarin masu amfani da POS maras rajista, inda ta ce hakan ya saɓa wa dokokin hukumar na shekarar 2020 da kuma dokar CBN ta aikin banki na agent.

Ta yi gargadi cewa ba za a bar wani mai gudanar da sana’ar POS ya yi aiki ba tare da rajistar CAC ba, inda ta ƙara cewa hukumomin tsaro za su tilasta bin doka a faɗin ƙasa.
Sanarwar ta ƙara jaddada cewa wannan sakacin, da masu gudanar da irin waɗannan sana’o’in ke yi na saka ‘yan Nijeriya da kasuwancinsu cikin hatsari inda ta ce dole ne a dakata.

“Jami’an tsaro za su ƙwace ko kuma rufe duk wani wurin sana’ar POS maras rajista,” in ji sanarwar.

Hukumar ta buƙaci duka masu amfani da POS ɗin su cika ƙa’idojin da suka kamata nan take.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#