Sport
Dollar
42,5354
0.07 %Euro
49,5729
-0.06 %Gram Gold
5.744,6300
-0.15 %Quarter Gold
9.538,1500
0.27 %Silver
79,8400
2.28 %Ƙasashen Afirka sun shiga cikin wani yanayi na sauya shirye-shiryensu bayan hukuncin da hukumar FIFA ta yanke na rage lokacin da ya kamata a saki ‘yanwasa zuwa ƙungiyoyinsu na ƙasa kafin soma Gasar Cin Kofin Afirka a wannan wata.
Kasa da makkonni uku a fara Gasar Cin Kofin Afrika ta 2026 a Morocco, daga 21 ga watan Disamba zuwa 18 ga Janairu, Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya ta sanar a ranar Laraba cewa ƙungiyoyi na buƙatar su saki ‘yan wasa ne kawai daga 15 ga Disamba maimakon makonni biyu kafin soma gasar cin kofin nahiyar, kamar yadda dokar FIFA ta tanada.
Senegal ta soke shirinta na atisayen 'yanwasa a ƙasar Tunisiya a cewar Majiyoyi, yayin da Angola da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da Mozambique da kuma zakarun da ke kare kambun Ivory Coast dole ke sake tunani kan shirye-shiryen da za a yi a Portugal da Sifaniya.
"Abin da ke da ban takaici da gajiyarwa shi ne tun lokacin da aka bude gasar cin kofin duniya a bara, muka soma kammala shirye-shirye," a cewar kocin Angola ɗan Faransa Patrice Beaumelle.
"Mun so mu buɗe sansanin atisaye a ranar 8 ga Disamba a yankin Algarve da ke kudancin Portugal. zuwa yanzu na kwashe wata ɗaya da rabi ina zuwa wurin. Mun shirya komai, mun yi aiki kan abubuwan da ke kunshe cikin horon, da wuraren da za a buga wasannin sada zumunci. Yanzu komai yana cikin haɗari.
""Dole ne mu kasance a Morocco a ranar 18 don yin wasa a ranar 22 ga watan nan." Don haka yanzu ba za mu iya sake kiransa sansanin horo ba," in ji shi.
Rashin girmamawa?
Za a soke wasannin sada zumunta da dama da aka shirya yi tsakanin ƙasashen duniya don share fagen gasar.
"Da farko mun so mu buga wasannin sada zumunta biyu, a ranakun 14 da 18 ga Disamba, amma yanzu za mu buga wasa ɗaya ne kawai, da kasar da har yanzu ba mu san wacece ba," in ji kocin Gabon Thierry Mouyouma.
Mafi yawan ƙasashe 24 da za su fafata a gasar Cin Kofin na Afirka sun kira 'yanwasansu ne daga ƙungiyoyin da suke wasa a Turai, waɗanda kuma galibi dole ne su sake su bayan ƙarshen wannan mako.
Hukumar FIFA ta ce an amince da gajeren lokacin sakin ‘yanwasan ne, kamar dai yadda aka yi a gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar, kana hakan ya biyo bayan tattaunawarta da Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka da sauran masu ruwa da tsaki don "rage tasirin ɓangarori daban-daban", ba tare da ƙarin bayani ba.
Ko da yake kocin ƙasar Mali Tom Saintfiet, ya ce hakan ya nuna rashin girmamawa ga ƙwallon ƙafa ta Afirka kuma FIFA ta ba wa ƙungiyoyin Turai fifiko.
Kazalika, kocin- koci sun soki sanarwar da aka yi a makare, la’akari da cewa an sanar da ranakun wasan ƙarshe na gasar cin kofin ƙasashen duniya a watan Yunin bara, wanda ya ba FIFA isasshen lokaci don yanke hukuncinta.
Comments
No comments Yet
Comment