Dollar

0,0000

%

Euro

0,0000

%

Gram Gold

0,0000

%

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kocin Real Madrid, Xabi Alonso ya ce ba shi da tababa kan cewa za su doke Manchester City a wasan Larabar nan na gasar Zakarun Turai.

Alonso ya ce ba ya shakkar Real Madrid za ta doke Man City

Za a fara buga wasannin gasar Zakarun Turai na mako na a shida ranar Talata da Larabar nan, 9 zuwa 10 ga Disamban 2025.

Cikin wasannin da za su ɗauki hankali akwai wasan Real Madrid da Manchester City, waɗanda kowannensu ya lashe gasar cikin shekaru uku na bayan nan.

Sai dai duka ƙungiyoyin biyu ba sa cikin yanayi mafi kyawu a ɓangaren tagomashi da lashe wasanni a gasannin ƙasashensu.

A Sifaniya, Madrid na mataki na 2 a teburin La Liga da maki 36 daga wasanni 16, inda a Ingila kuma Man City take mataki na 2 da maki 31 daga wasanni 15 a teburin Firimiya.

A gasar ta UEFA kuwa, bayan buga wasanni biyar a kakar bana, Madrid tana mataki na 5 da maki 12, sai City da take mataki na 9 da maki 10.

Sai dai a yayin da Alonso ya gaza cin wasa huɗu cikin biyar da ya jagoranta a kwanakin nan, kocin ya sha alwashin doke City a wasansu na gaba.

Manta baya

Xabi Alonso ya dage kan cewa tawagarsa ta manta baya kan batun rashin nasararsu a hannun Centa Vigo ranar Lahadin da ta gabata da ci 2-0.

A yanzu sun samu ƙwarin gwiwar fuskantar Manchester City, inda kuma ya yi watsi da batun cewa gidansa akwai rashin jituwa tsakanin ‘yanwasa.

Baya ga rashin nasara, Alonso na fuskantar rashin ‘yanwasan da ke fama da jinya, ciki har da Eder Militao da David Alaba da Dani Carvajal.

Duk da zai kara ne da zaƙaƙurin koci Pep Guardiola, Alonso ya ce ba ya kallon wasan a matsayin wanda zai kawo masa matsala.

Sai dai masu sharhi da yawa na ganin wasan zai iya zama wanda zai yanke hukuncin kan makomar Alonso, wanda a yanzu yake kakarsa ta farko a Real Madrid.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#