Sport
Dollar
42,8324
0.03 %Euro
50,6727
0.54 %Gram Gold
6.162,1600
0.86 %Quarter Gold
10.205,2300
2.31 %Silver
97,6500
2.96 %Tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya da aka sani da 'Super Eagles' za ta fuskanci tawagar ƙwallon ƙafa ta Tanzania da aka sani da 'Taifa Stars', a yau 23 ga Disamba 2025 a gasar AFCON 2025.
A ranar Talata ne tawagogin ƙwallon ƙafa na Nijeriya da na Tanzania za su fuskanci juna a wasansu na farko na gasar ƙasashen Afirka mafi girma ta AFCON 2025 a Maroko.
Wasan na Rukunin C shi ne na tawagar 'Taifa Stars',a karo na huɗu a tarihin ƙwallon ƙafarta. Tanzania ba ta taɓa samun nasara a gasar AFCON a lokutan da ta halarta na 1980, 2019 da 2024 ba.
A duka lokuta uku da Tanzania ta halarci AFCON, ba ta taɓa yin nasara ba saboda ana fitar da ita tun a matakin rukuni.
A cikin wasanni bakwai da aka buga tsakanin Nijeriya da Tanzania a tarihi, Nijeriya ta doke Tanzania a wasanni huɗu, sun yi canjaras sau uku, amma Tanzania ba ta sami nasara ba ko ɗaya ba.
“Duk da yanayin da muke ciki mai wahala, mun zaɓi nasara. Mun san 'yan Nijeriya, mun riga mun buga da 'yan Uganda kuma mun san su sosai, har ma mun san 'yan Tunisia”, in ji Mataimakin Ministan Harkokin Labarai, Al'adu, Nishaɗi da Wasanni na Tanzania, Paul Makonda, bayan ya gana da tawagar 'Taifa Stars' a Barcelo Convention Center, birnin Fes, Maroko, inda tawagar ta kafa sansanin shiri.
Yanzu haka, fatan jama'ar Tanzania shi ne ganin 'Taifa Stars' sun samu nasara a wannan wasa mai muhimmanci na Rukunin C, yayin da muke sa ido kan sakamakon wasan Uganda da Tunisia.
Wannan wasa zai kasance mai muhimmanci ga Tanzania, kasancewarsu za su kasance masu masaukin baƙi tare da haɗin gwiwa da Kenya da Uganda a gasar AFCON ta 2027.
Comments
No comments Yet
Comment