Dollar

42,8585

0.06 %

Euro

50,8450

0.17 %

Gram Gold

6.219,6700

0.43 %

Quarter Gold

10.205,2300

0 %

Silver

98,9500

0.45 %

Hukumomin Turkiyya sun ce an daina jin ɗuriyar jirgin saman na Falcon 50 wanda yake na haya ne da ke kan hanyar zuwa Tripoli bayan ya bayar da rahoton wata matsala a kusa da tsakiyar Turkiyya.

Babban hafsan sojin Libya da jami'ai sun mutu a hatsarin jirgin sama a kusa da Ankara: Dbeibah

Firaministan Libya, Abdulhamid Dbeibeh, ya sanar da rasuwar babban hafsan sojin ƙasar da wasu manyan jami'ai sakamakon wani mummunan hatsari yayin da suke komawa gida daga wata ziyarar aiki a Turkiyya.

A wani saƙo a shafinX, Dbeibeh ya ce a ranar Talata ya karɓi labarin “cike da jimami da baƙin ciki,” yake tabbatar da rasuwar Laftanar Janar Mohammad al-Haddad da jama’ar da ke cikin tawagarsa.

Cikin waɗanda suka mutu tare da al-Haddad akwai hafsan rundunar sojan ƙasa, da shugaban masana'antar kayayyakin soji, da wani mai bai wa babban hafsan shawara, da mai ɗaukar hoto na ofishin yada labarai.

Firaministan ya ce hatsarin ya faru ne a lokacin dawowarsu daga babban birnin Turkiyya, Ankara, ba tare da ya bayar da ƙarin bayani kan abin da ya haifar da haɗarin ba.

Ya bayyana cewa wannan babban rashi ne ga ƙasa da rundunonin soji, kuma ya ce Libya ta rasa maza da suka yi wa ƙasarsu hidima da “gaskiya, ladabi da ƙwazo,” yana mai miƙa ta'aziyya ga iyalansu, da abokan aikin su sojoji da jama'ar Libya baki ɗaya.

Ministan Cikin Gida na Turkiyya, Ali Yerlikaya, ya ce tun a farko an gano ɓaraguzan jirgin na haya da ya tashi zuwa Libya wanda ke ɗauke da babban hafsan sojin bayan ya tashi daga Ankara, a gundumar Haymana ta Ankara.

Ministan na Turkiyya ya ce an rasa hanyoyin sadarwa da jirgin da ke ɗauke da shugaban sojin na Libya ba daɗewa bayan tashinsa daga filin jirgin Esenboga na Ankara.

Jirgin na haya na nau'in Falcon 50 mai lambar 9H-DFJ ya tashi da misalin ƙarfe 8:10 na dare agogon Turkiyya (5:10 agogon GMT) yana neman zuwa Tripoli. Sadarwa ta katse kusan ƙarfe 8:52 na yamma a lokacin gida (1752 GMT), kamar yadda Yerlikaya ya bayyana a dandalin sada zumunta na Turkiyya NSosyal.

Ya bayyana cewa jirgin ya aike da sanarwar saukar gaggawa kusa da Haymana, wata gunduma da ke kudu da babban birnin Ankara.

'Tun daga nan, ba a sake samun jin ɗuriyar jirgin ba bayan saƙon na gaggawa da ya tura tun da farko,' in ji shi.

A cewar ministan, fasinjoji biyar ne ke cikin jirgin, ciki har da al-Haddad.

Gidan talabijin na Turkiyya, NTV, ya ruwaito cewa an rasa sadarwa da jirgin na haya da aka amince yana ɗauke da al-Haddad a sararin babban birnin, yayin da bayanan bin diddigin jiragen sama suka nuna an karkatar da wasu jirage daga filin Esenboga a matsayin matakin taka tsan-tsan.

Ma'aikatar tsaron Turkiyya ta sanar a baya cewa babban hafsan sojin na Libya na ziyara a Ankara, inda ya gana da takwaransa na Turkiyya da wasu manyan kwamandojin soja. Ziyarar na cikin matakin haɗin gwiwar soji da ta tsaro da ke gudana tsakanin kasashen biyu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#