Dollar

42,1247

0.06 %

Euro

48,7571

0.72 %

Gram Gold

5.399,5600

0.14 %

Quarter Gold

9.158,9600

1.15 %

Silver

65,2600

0.15 %

An rantsar da shi a wani biki da aka gudanar a majalisar dokoki a babban birnin kasar, Yaounde, don fara sabon wa’adin shekaru bakwai a shugabancin wannan kasa ta tsakiyar Afirka.

Paul Biya na Kamaru: An rantsar da shugaban da ya fi tsufa a duniya a karo na 8 a mulki

An rantsar da Paul Biya, wanda ya kasance shugaban kasar Kamaru tsawon shekaru 43 a ranar Alhamis don wa’adin shugabanci na takwas, bayan wani zabe mai cike da takaddama wanda ya haifar da zanga-zangar jama’a inda mutane da dama suka rasa rayukansu.

Biya mai shekaru 92, wanda shi ne shugaban kasa mafi tsufa a duniya, ya lashe zaben ranar 12 ga Oktoba da kashi 53.7 cikin dari na kuri’u, bisa ga sakamakon hukuma, yayin da babban abokin hamayyarsa, tsohon ministan gwamnati Issa Tchiroma Bakary, ya samu kashi 35.2 cikin 100.

An rantsar da shi a wani biki da aka gudanar a majalisar dokoki a babban birnin kasar, Yaounde, don fara sabon wa’adin shekaru bakwai a shugabancin wannan kasa ta tsakiyar Afirka.

"Ba zan yi kasa a gwiwa ba wajen tabbatar da cewa na cancanci wannan amana," in ji Biya ga taron da ya samu halartar manyan 'yan siyasar cikin gida amma babu shugabannin kasashen waje.

"Na fahimci girman matsalolin da kasarmu ke fuskanta. Na fahimci yawan kalubale da tsanani da muke fuskanta, kuma na fahimci zurfin takaicin jama’a da kuma girman burinsu," ya kara da cewa.

Zabe mai cike da takaddama

Tchiroma, tsohon abokin Biya da ya koma bangaren adawa, ya ja hankalin matasa masu kada kuri’a kuma har yanzu yana dagewa cewa shi ne ya lashe zaben, wanda ya kasance mai matukar karfi fiye da yadda aka zata.

An ruwaito cewa mutane da dama sun mutu lokacin da jami’an tsaro suka dakile zanga-zangar adawa kafin da kuma bayan sanar da nasarar Biya a ranar 27 ga Oktoba.

Tchiroma tun daga lokacin ya bukaci magoya bayansa su gudanar da “abin da ya dace,” inda aka rufe shaguna da dakatar da wasu ayyukan jama’a.

Mutane sun amsa wannan kira ta hanyoy mabambanta, inda aka bi umarnin sosai a Garoua da Douala, amma a Yaounde mafi yawan shaguna sun kasance a bude, yara suna makaranta, kuma ma’aikata suna zuwa aiki.

Tchiroma ya kasance a killace a gidansa a Garoua bayan sanar da sakamakon, amma a ranar Talata, daya daga cikin masu magana da yawunsa ya shaida wa AFP cewa yana "kan tafiya."

Zarge-zarge kan Tchiroma

Gwamnati ta ce tana shirin fara shari’a kan shugaban adawar, tana zargin shi da "kiran juyin juya hali a kai a kai."

Ta amince cewa mutane sun mutu a rikicin, amma ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu ba.

Kungiyar Tarayyar Turai da Kungiyar Tarayyar Afirka duk sun yi Allah wadai da yadda mahukuntan suka yi amfani da karfi wajen dakile zanga-zangar, yayin da Kwamishinan Kare Hakkin Dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya bukaci a gudanar da bincike.

Biya shi ne mutum na biyu kawai da ya jagoranci Kamaru tun samun ‘yancin kai daga Faransa a shekarar 1960.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#