Sport
Dollar
42,0996
0.02 %Euro
48,3664
0 %Gram Gold
5.386,3300
1.05 %Quarter Gold
9.055,1100
0.33 %Silver
65,1700
2.12 %Hukumar Majalisar Dinkin Duniya kan gudun hijira ta ƙiyasta cewa tuni fiye da mutane 38,000 suka tsere daga yankin Arewa da Kudancin Kordofan.
Aƙalla mutane 40 ne suka mutu a wani harin jirgin sama mara matuƙi da rundunar RSF ta kai a yankin Kordofan ta Arewa da ke tsakiyar Sudan, a cewar wani jami’in yankin.
Kwamishinan harkokin jinƙai na yankin Kordofan ta Arewa, wanda ba a bayyana sunansa ba, ya shaida wa kafar Al Jazeera a ranar Litinin cewa mace-macen sun faru ne a harin da aka kai wa fararen hula a ƙauyen Al Luweib da ke gabashin babban birnin lardin El Obeid.
A baya gwamnatin jihar ta ce an kashe fararen hula da dama, ciki har da yara da mata, a harin da aka kai wa wani tantin zaman makoki a ƙauyen.
Ta bayyana harin a matsayin wani "sabon laifi kan irin zaluncin da RSF ke ci gaba yi wa fararen hula", tana mai cewa mata, yara da tsofaffi da dama suna cikin waɗanda abin ya shafa, ko da yake ba ta bayyana ainihin adadin mutanen ba.
Gwamnatin jihar ta yi kira ga al'ummar duniya da su gaggauta ayyana RSF a matsayin "ƙungiyar ta'addanci", tana mai zarginta da "aikata laifukan kisan kare-dangi kan fararen hula marasa makamai".
Harin dai ya zo ne jim kadan bayan da RSF ta ce, ta kusa kai hari El Obeid, "inda ta yi kira ga mazauna yankin da su bar birnin" ta hanyar abin da ta kira hanyoyin tsaro.
Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Duniya (IOM) ta ƙiyasta cewa fiye da mutane 38,000 sun tsere daga Arewa da Kudancin Kordofan saboda tabarbarewar tsaro a yankin tun daga ƙarshen watan Oktoba.
Rundunar RSF ta karɓe iko da birnin Bara da ke Kordofan ta Arewa a matsayin wani bangare na yakin da take yi da sojojin Sudan, ko da yake ta musanta cewa ta kai hari kan fararen hula.
A ranar 26 ga watan Oktoba, RSF ta kwace birnin Al Fasher, babban birnin jihar Darfur ta Arewa, kana ta aikata kisan gilla kan fararen hula, a cewar ƙungiyoyin cikin gida da na ƙasashen waje, kazalika hakan ya biyo bayan gargadin cewa harin na iya janyo rabewar yankin Sudan.
Tun dai daga ranar 15 ga Afrilun 2023, ƙasar Sudan ta fada yaƙin da har yanzu masu shiga tsakani daga yankin da ƙasashen waje suka gaza kawo ƙarshensa.
Comments
No comments Yet
Comment