Sport
Dollar
0,0000
%Euro
0,0000
%Gram Gold
0,0000
%Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaba Trump ya nanata zargin cewa Afirka Afirka Ta Kudu ta ƙwace filaye, duk da cewa mahukunta a Pretoria sun musanta iƙirarin.
Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana ranar Laraba cewa ya kamata a cire ƙasar Afirka ta Kudu daga cikin ƙasashen G20 sannan ya ce ba zai halarci taron da za a yi a ƙasar ba.
"Bai kamata Afirka Ta Kudu ta ci gaba da kasancewa cikin G20 ba saboda abin da ya faru a wancan wajen ya yi muni sosai," kamar yadda Trump ya shaida wa taron ‘yan kasuwar Amurka a Miami.
"Ba zan je ba ... ba zan wakilci ƙasarmu a can ba. Bai kamata ta kasance a yi taron a ƙasar ba," kamar yadda ya bayyana, inda yake magana game da taron G20 a Johannesburg wanda ake shirin yi tsakanin ranar 22 zuwa 23 na watan Nuwamba.
Mataimakin shugaban ƙasa J.D. Vance ne ake sa ran zai halarci taron.
Trump yana zargin Afirka Ta Kudu da ƙwace filaye da kuma yin “ba daidai ba ga wasu mutane," lamarin da ya kira "tauye haƙƙin ɗan’adam mai yawa”.
Trump ya ba da umarni na 14204 a watan Fabrairu, inda ya bai wa hukumomin gwamnatin tarayyar ƙasar umarnin sake tsugunar da fararen-fata ‘yan ƙabilar Afrikaan na Afirka Ta Kudu, inda ya bayyana su “ a matsayin waɗanda aka yi wa wariyar launin fata mara adalci," kuma ya janye tallafin da Amurka ke bai wa Afirka Ta Kudu.
Gwamnatin Afirka Ta Kudu ta yi watsi da iƙirarin Trump, tana mai cewa sun "dogara ne kan wani zato da bai dace da gaskiya ba."
Comments
No comments Yet
Comment