Sport
Dollar
41,2717
0.05 %Euro
48,4417
-0.26 %Gram Gold
4.836,4900
0.28 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ƙungiyar NUPENG ta yi shelar cewa za ta fara yajin aiki daga ranar Litinin, 8 ga watan Satumbar shekarar 2025, kan zargin da ta yi wa kamfanin Dangote cewa yana ɗaukar matakan da suka saɓa wa dokokin ƙwadago.
Zaman sirrin da Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta gudanar ranar Litinin da maraice domin sulhuta ƙungiyar ma’aikatan dakon man fetur da gas (NUPENG) da kamfanin mai na Dangote ya kasa cim ma nasara.
Rahotanni daga Nijeriya sun ce zaman da Ministan Ƙwadagon ƙasar, Mohammed Dingyadi, da Ƙaramar Ministar Ƙwadago, Nkiruka Onyejeocha, suka jagoranta wani mataki ne na warware taƙaddamar da ke tsakanin ɓangarorin biyu domin kauce wa yajin aikin da ƙungiyar NUPENG ta ce za ta yi.
Waɗanda suka halarci zaman sun haɗa da shugabannin ƙungiyar NUPENG da jami’an ƙungiyar ƙwadagon Nijeriya (NLC) da kuma na ƙungiyoyin ƙwadago na TUC.
Kazalika zaman ya samu halartar babban daraktan ajiya da rabawa da sayar da mai na hukumar da ke kula fannin tacewa da sayar da mai ta Nijeriya (NMDPRA), Ogbugo Ukoha, da kuma wakilan kamfanin Dangote da gidan man MRS.
Sai dai an kammala taron ba tare da cim ma matsaya ba game da taƙaddamar da ake yi tsakanin NUPENG da Matatar Mai ta Dangote.
Ranar Juma’ar da ta gabata ne dai ƙungiyar ƙwadagon NUPENG ta yi shelar ƙaddamar da yajin aiki daga ranar 8 ga watan Satumba kan abin da ta kira ƙoƙarin Matatar Man Dangote na hana direbobin tankokin dakon mai na CNG ɗinsa shiga ƙungiyoyin ƙwadago.
Comments
No comments Yet
Comment