Sport
Cocin Katolika reshen Kafanchan ta ce mutum goma ne aka sace, amma ‘yansanda sun ce biyar ne, sannan mutanen da aka kashe biyu sojoji ne ɗaya kuma ɗansanda.
‘Yanbindiga sun kashe mutane uku kuma sun sace wani faston Katolika da wasu mutane yayin wani harin da suka kai a da sanyin safiya a gidan faston a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, in ji majiyoyin coci da 'yan sanda a ranar Lahadi.
Harin wanda aka kai a ranar Asabar a Ƙaramar Hukumar Kauru ya nuna yadda rashin tsaro ke ƙara ƙaruwa a yankin, kuma ya zo 'yan kwanaki bayan jami'an tsaro sun kuɓutar da duka masu ibada 166 da aka sace a hare-haren da ‘yanbindiga suka kai kan wasu coci biyu a wasu sassa na Kaduna.

Harin asubahi
Cocin Katolika reshen Kafanchan ta bayyana cewa limamin da aka sace shi ne Nathaniel Asuwaye, wanda fasto ne a cocin Holy Trinity Catholic Church a Karku, kuma ta ce wasu mutane 10 an sace su.
An kashe mazauna uku yayin harin, wanda ya fara kusan karfe 3:20 na safe (0220 GMT), in ji sanarwar cocin.
Wani mai magana da yawun 'yansandan Kaduna ya tabbatar da lamarin, amma ya ce mutum biyar ne aka sace gaba ɗaya kuma mutane ukun da aka kashe jami’an tsaro ne,
"Jami'an tsaro sun yi musayar wuta da 'yanbindiga, sun kashe wasu daga cikinsu, kuma abin takaici sojoji biyu da ɗansanda sun rasu," in ji shi.
Sakon hadin kai daga Fafaroma
Fafaroma Leo, a lokacin jawabin mako-makonsa ga mabiya a Filin St. Peter, ya nuna goyon bayansa kan waɗanda ɓarayi ke kai wa hari a Nijeriya.
"Ina fatan hukumomin da suka dace za su ci gaba da aiki da zuciya don tabbatar da tsaro da kare rayuwar kowanne ɗan ƙasa," in ji Leo.
Comments
No comments Yet
Comment