Yan bindiga sun farmaki kasuwanni biyu a yankin Kwande cikin kwanaki kaɗan

Hare-hare biyu sun kashe mutum 30 a jihar Benue

Hare-hare biyu da aka kai cikin ’yan kwanaki kaɗan sun yi sanadin mutuwar mutum 30 a wasu garuruwa biyu makwabta a jihar Benue da ke tsakiyar Nijeriya, jihar da ta daɗe tana fama da rikicin kabilanci da na albarkatun ƙasa, a cewar majiyoyi. TRT Hausa

A yammacin ranar Juma’a, ’yan bindiga sun kashe aƙalla ’yan kasuwa 13 a kasuwar Anwase da ke yankin Kwande, inda jami’in ƙaramar hukuma Ibi Andrew ya ce maharan sun buɗe wuta kan mutane ba tare da nuna bambanci ba, lamarin da ya haddasa firgici da asarar dukiya. TRT Hausa

Kafin hakan, a ranar Talata, wasu maharan ɗauke da makamai sun kai hari kasuwar Mbaikyor da ke kusa, inda suka kashe mutane 17 ciki har da wani jami’in ɗansanda, kamar yadda wasu mazauna ƙauyen suka tabbatar. TRT Hausa

Yankin ya dade yana fuskantar tashin hankali tsakanin makiyaya Fulani da al’ummomin manoma, rikicin da ya samo asali daga takaddamar filaye, ƙarancin albarkatu da sauyin yanayi, tare da yawaitar makamai da kuma raunin martanin gwamnati. TRT Hausa

 
 
 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#