Sport
Dollar
40,4343
0.24 %Euro
47,1614
0.49 %Gram Gold
4.349,9900
0.54 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Jama’ar arewacin Nijeriya, musamman dalibai da tsaffin daliban jami’ar ta UNIMAID, da ‘yan Jihar Borno, suna tofa albarkacin bakinsu kan sauya sunan jami'ar UNIMAID zuwa sunan Muhammadu Buhari.
Muhawara ta ɓarke a shafukan sada zumunta bayan da gwamnatin tarayyar Nijeriya ta ayyana sauya sunan jamia’r Maiduguri daga “University of Maiduguri” zuwa “Muhammadu Buhari University, Maiduguri”.
Shugaban Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ayyana sauyin yayin wani taro na musamman na majalisar zartarwar ƙasa da aka gudanar ranar Alhamis.
Jama’ar arewacin Nijeriya, musamman ɗalibai da tsaffin ɗaliban jami’ar ta UNIMAID, da ‘yan Jihar Borno, suna tofa albarkacin bakinsu kan lamarin.
Labarin ya samu yabo bisa cewa marigayi Buhari ya ziyarci jihar Borno sama da kowace jiha a zamanin mulkinsa. Kuma akwai tarin ‘yan asalin jihar Borno da ya naɗa a manyan muƙamai a gwamnatinsa.
Sannan a tarihi, Manjo Janar Buhari ne gwamnan mulkin soja na farko na Jihar Borno, kuma ya yi aiki tuƙuru don daƙile matsalar rikicin Boko Haram.
Masu ganin dacewar sauyin sunan jami’ar, suna ganin babu wani aibu game da sauyin zai yi ga daraja ko ingancin karatu a jami’ar, kasancewar sunanta ne kawai ya canja.
A shafin Facebook, wani toshon ɗalibin UNIMAID, mai sun Alkali Adamu Askira ya wallafa saƙon bidiyo don murnar sanya sunan Muhammadu Buhari ga jami’ar ta UNIMAID.
Saƙon na cewa tshohon ɗalibin a shirye yake ya maido da satifiket ɗinsa na jami’ar har ma ya biya kuɗi don a ba shi sabon satifiket mai ɗauke da sabon sunan jami’ar.
Sake tunani
Batu na farko da masu sukar lamarin ke magana a kai shi ne, tuntuni akwai makarantu da cibiyoyi a jihar ta Borno da aka sanya wa sunan marigayi Muhammadu Buhari.
A jihar akwai filin jirgin sama na Muhammadu Buhari Airport, da makarantar Muhammadu Buhari Mega School, da cibiyar lafiya ta Muhammadu Buhari Trauma Centre da ke cikin asibitin koyarwa na jami’ar ta UNIMAID, da ma ginin shugaban jami’ar.
Don haka ne suke shawartar shugaba Tinubu ya sake tunani kan wannan hukunci, saboda ba sa son su sauya taken jami’ar na “If you want to be made, come to Unimaid”.
Masu ƙorafin suna cewa akwai tarin ɗalibai da tsaffin ɗaliban UNIMAID da abin bai musu daɗi ba, ko da kuwa ba su fito sun soki batun ba saboda alhinin rasuwar shugaba Buhari.
Wani mai sharhi a shafin Facebook, Sodiq Alabi, ya wallafa cewa “Na so a ce ba a sanya sunan GMB [Muhammadu Buhari] ga wata jami’a ba, amma idan ma sai an yi, ya kamata BAT [Shugaba Tinubu] ya sanya sunan abokinsa a wasu makaranytun '[ba UNIMAID ba].”
Cikin makarantu da ake ba da misalin cewa sun cancanci sunan marigayi Muhammadu Buhari, akwai Federal University of Transportation Daura, Nigerian Army University Biu, Federal University Dutsinma, Federal University of Technology, Babura, da sauransu.
A yanzu dai, fatan masu neman a sake tunani kan sauya sunan UNIMAID, shi ne abin da ya faru a zamanin shugaba Goodluck Jonathan da ya yi amai ya lashe a ƙoƙarinsa na sauya sunar Jami’ar Lagos daga UNILAG zuwa MKO Abiola University.
Comments
No comments Yet
Comment