Sport
Dollar
40,2611
0.13 %Euro
46,8110
0.22 %Gram Gold
4.311,5500
0.33 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban Nijeriya Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da Firaministan Nijar Ali Lamine Zaine da tsohon shugaban Nijar Mahamadou Issoufou na daga dubban mutanen da suka halarci jana'izar a birnin Daura da yammacin Talata.
An gudanar da jana’izar tsohon shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari a gidansa da ke birnin Daura na Jihar Katsina a arewacin ƙasar.
An binne gawar marigayi Muhammadu Buhari ne da misalin karfe shida na yamma a agogon Nijeriya bayan kai ta Daura daga filin jirgin saman birnin Katsina.
Buhari ya rasu ne a birnin Landan ranar Lahadi yana da shekaru 82 a duniya.
Dubban mutane ne suka halarci jana’izar a karkashin sanya idon shugaban Bola Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima da sauran manyan mutane daga ciki da wajen Nijeriya.
Comments
No comments Yet
Comment