Dollar

39,1781

-0.14 %

Euro

44,7903

0.16 %

Gram Gold

4.234,8400

2.07 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Kwamishinan Harkokin Matasa da Wasanni na Jihar Kano Mustapha Rabiu Kwankwaso ne ya tabbatar da batun hatsarin a ranar Asabar inda a cikin alhini ya tabbatar da mutuwar mutanen.

Motar tawagar ‘yan wasan Kano ta yi hatsari, mutum 21 sun rasu

Ɗaya daga cikin motocin da ke ɗauke da ‘yan wasan Kano waɗanda suka je bikin wasanni a Jihar Ogun ta yi hatsari, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 21.

Kwamishinan Harkokin Matasa da Wasanni na Jihar Kano Mustapha Rabiu Kwankwaso ne ya tabbatar da batun hatsarin a ranar Asabar inda a cikin alhini ya tabbatar da mutuwar mutanen.

Kwamishinan ya bayyana cewa daga cikin waɗanda suka rasu akwai ‘yan wasa da masu kula da su.

Ya bayyana cewa gwamnatin Kano na abin da ya dace wurin ganin mamatan an kai su ga iyalansu sannan marasa lafiya sun samu kulawa yadda ya dace.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#