Dollar

39,2381

-0.04 %

Euro

44,7677

0.11 %

Gram Gold

4.232,8800

2.02 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Hukumar EFCC a ƙasar ta ce kotun ta ɗaure mutanen 15 kan samunsu da laifin “ta’addanci ta intanet da kuma amfani da intanet ɗin domin aikata zamba cikin aminci".

Kotu a Nijeriya ta ɗaure mutum 15 'yan ƙasashen waje

Wata kotu a Nijeriya ta ɗaure mutum 15 ‘yan ƙasashen waje kan samunsu da laifin “ta’addanci ta intanet da kuma amfani da intanet ɗin domin aikata zamba cikin aminci,” kamar yadda hukumar EFCC ta bayyana.

Wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Dele Oyewale ya fitar ta bayyana cewa mutanen sun ƙunshi ‘yan ƙasar Philipines 11 sai ‘yan ƙasar China biyu sai ɗan ƙasar Indonesia ɗaya da kuma ɗan Malaysia ɗaya waɗanda dukansu suna a Legas.

Duka mutanen an yanke musu hukuncin zaman gidan yari na shekara ɗaya tare da biyan tarar naira miliyan ɗaya kowanensu.

Haka kuma kotun ta bayar da umarni a ƙwace na’urorin da ke hannun mutanen domin miƙa su ga gwamnatin tarayya.

Hukumar ta EFCC ta bankaɗo ɓoyayyun wurare da dama da matasa ke koyon zamba a ƙasar.

Haka kuma ƙwararru da ke sharhi kan aikata laifuka ta intanet sun yi gargaɗin cewa akwai ‘yan ƙasashen waje da dama waɗanda suka ƙware ta ɓangaren zamba ta intanet da suka tare a Nijeriya domin damfarar jama’a.

Ko a watan Disamba sai da hukumar EFCC ta kama mutum 792 a wani samame guda ɗaya da aka gudanar a unguwar Victoria Island da ke Legas.

Hukumar ta ce aƙalla 192 daga cikin waɗanda ake zargin ‘yan ƙasashen waje ne – 148 daga cikinsu ‘yan China ne.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#