Dollar

39,2105

-0.08 %

Euro

44,7791

0.14 %

Gram Gold

4.233,0900

2.03 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Binciken wucin-gadi da EFCC ta yi ya nuna cewa mutanen biyu na hanyar kai wa wani boka dalolin na jabu wanda ya yi iƙirarin cewa zai mayar da su daloli na ainahi.

EFCC ta kama mutum biyu a Kano da fiye da dala dubu 800 ta ‘bogi’

Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Zagon Ƙasa ta Nijeriya EFCC ta kama wasu mutum biyu da dala 899,800 wadda ake zargin ta bogi ce.

A wata sanarwa da hukumar ta fitar a ranar Asabar, ta bayyana cewa tuni ofishinta na Kano ya ƙaddamar da bincike kan mutanen biyu da aka kama da dalolin.

Waɗanda ake zargin sun haɗa da Abubakar Hussaini mai shekara 42 da Sahabi Adamu mai shekara 53 waɗanda tun da farko jami’an hukumar NDLEA da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ne suka kama su a Wudil.

An kama su ne a cikin wata mota ƙirar Golf 3 a hanyarsu ta zuwa ƙauyen Kila da ke Ƙaramar Hukumar Gwaram da ke Jigawa.

Binciken wucin-gadi da aka gudanar ya nuna cewa mutanen na kan hanyar zuwa ƙauyen Kila ne domin haɗuwa da wani mutum mai suna Muhammad Walo wanda ya haɗa su da Mallam Mashiru, wanda boka ne da ke iƙirarin mayar da dala ta jabu zuwa dala ta ainahi.

EFCC ta ce za a gurfanar da mutanen a gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#