Dollar

39,1845

-0.03 %

Euro

44,8175

-0.16 %

Gram Gold

4.234,0200

-0.67 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Hukumar ta bayyana cewa bayan bayanan sirrin da ta samu, sai jami’anta suka sa na’ura ta duba mutanen da ake zargi inda aka tabbatar suna ɗauke da hodar ibilis ɗin. Sai aka saka musu ido har sai da kowanen su ya yi kashin ɗauri 45 na hodar ibilis.

Maniyyatan Aikin Hajji biyu sun yi kashin ɗauri 90 na hodar Ibilis a Kano

Hukumar NDLEA a Nijeriya da ke yaƙi da fataucin miyagun ƙwayoyi ta sanar da kama wasu mutum biyu maniyyatan Aikin Hajji waɗanda suka yi yunƙurin safarar hodar ibilis zuwa Saudiyya.

Hukumar ce ta tabbatar da hakan a wata sanarwar da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce baya ga kama maniyyatan, ta kama wasu ƙarin mutum biyu waɗanda su ne shugabannin gungun wata ƙungiyar da ke safarar ƙwayoyi zuwa Saudiyya.

NDLEA ɗin ta ce tun da farko ta kama Ibrahim Umar Mustapha da Muhammad Siraj Shifado a filin jirgin Malam Aminu Kano a daidai lokacin da suke shirin shiga jirgin Ethiopia domin tafiya Aikin Hajji.

Hukumar ta bayyana cewa bayan bayanan sirrin da ta samu, sai jami’anta suka sa na’ura ta duba mutanen da ake zargi inda aka tabbatar suna ɗauke da hodar ibilis ɗin. Sai aka saka musu ido har sai da kowanen su ya yi kashin ɗauri 45 na hodar ibilis, inda aka samu jimillar ɗauri 90 mai nauyin kilo 1.04.

Bayan zurfafa bincike, sai hukumar ta gano gungun masu safarar da shugabanninsu waɗanda suka ƙware wurin aika haramtattun kayayyaki Saudiyya.

NDLEA ta ce ta kama Abubakar Muhammad da Abdulhakeem Muammed Tijjani da kuma Muhammad Aji Shugaba a Kano waɗanda dukansu sun sun gawurta a wannan harka.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#