Sport
Dollar
40,6855
0.08 %Euro
47,1705
0 %Gram Gold
4.394,4500
-0.02 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ankara ta kuma yi tur da harin da aka kai Masallacin Kudus a yankin Gabashin Kudus da Yahudawa 'yan kama wuri zauna da kuma ministocin Isra'ila suka mamaye.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya yi wata tattaunawa ta waya da takwaransa na Masar, Badr Abdelatty, domin lalubo hanyoyin isar da tallafin jinƙai zuwa Gaza da kuma cim ma tsagaita wuta.
A cewar majiyoyin diflomasiyyar Turkiyya a ranar Lahadi, Fidan da Abdelatty sun tattauna kan mawuyacin halin jiƙai da ake ciki a Gaza, musamman kokarin magance yunwa mai tsanani da ake fama da ita sakamakon takunkuman Isra'ila, da kuma ci gaban tattaunawar tsagaita wuta.
Turkiyya ta yi Allah wadai da farmakin Isra'ila kan Masallacin Ƙudus.
Turkiyya ta yi kakkausar suka kan kwanton bauna da ministocin Isra'ila da jami'an tsaro, da wasu kungiyoyin ‘yan kama wuri zauna suka kai a Masallacin Ƙudus da ke gabashin Birnin Kudus da aka mamaye.
A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a ranar Lahadi, ta bayyana cewa irin wadannan matakai suna barazana ga tsaron Masallacin Ƙudus kuma suna yi wa ƙimar tsarkin birnin barazana, tana mai cewa wannan batu ba wai na yankin kawai ba ne, har ma da “lamarin lamirin bil’adama gaba daya.”
“Tayar da hankali da Isra'ila ke yi a kai a kai da kuma kiran da take yi na mamaye wasu yankuna, kai tsaye barazana ce ga ƙoƙarin samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu da ake yi, kuma suna lalata ƙoƙarin samar da zaman lafiya,” in ji ma’aikatar.
Turkiyya ta sake jaddada kiran da ta yi na a gaggauta tsagaita wuta a Gaza, tare da yin kira ga al’ummar duniya su goyi bayan samar da zaman lafiya mai dorewa bisa mafita ta kasashe biyu.
Comments
No comments Yet
Comment