Dollar

40,7015

0.02 %

Euro

47,2204

1.43 %

Gram Gold

4.394,9300

2.22 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Shugaban Turkiyya ya yi tur da hare-haren da Isra'ila ke cigaba da kai wa kan Falasɗinawa fararen hula a Gaza, musamman na yanayin matsananciyar yunwar da ta haddasa a can.

Dole al'ummar duniya su yi aiki don don dakatar da cin zalin Isra'ila a Gaza: Erdogan na Turkiya

Shugaban Ƙasar Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya yi kira ga duniya baki ɗaya da ta dauki matakin gaggawa don kawo ƙarshen hare-haren Isra'ila a Gaza da kuma bai wa agajin jinƙai fifiko ga yankin da aka killace, yana gargadin cewa ɗan’adam yana gab da rasa sanin ya kamatansa.

Da yake magana a yayin taron manema labarai tare da Shugaban Gabon, Brice Oligui Nguema, Erdogan ya ce, “Babban fifikonmu shi ne tabbatar da cewa agajin jinƙai ya isa ga 'yan'uwanmu a Gaza.”

“A matsayinmu na wakilan ɗan’adam, dole ne mu yi duk abin da ya dace don dakatar da wannan zalunci,” in ji shi.

Shugaban Turkiyya ya yi Allah wadai da ci gaba da hare-haren da Isra'ila ke kai wa kan fararen hula na Falasɗinu, musamman a cikin yanayin yunwa da wahalhalu da ake fuskanta a Gaza.

“Duk wanda ke da ɗan sauran lamiri ko tausayi, ko mutunci yana gab da rasa su ƙarƙashin nauyin wannan zalunci,” in ji shi.

“Ba wanda zai iya yin shiru a gaban yanayin da yara marasa laifi ke mutuwa saboda yunwa, kuma fararen hula da ke taruwa don neman agajin abinci ake harbi da gangan.”

Matsin lamba ga Isra'ila

Erdogan ya kara da cewa Turkiyya za ta ƙara ƙaimi a kokarin diflomasiyya a cikin kwanaki masu zuwa don kara matsin lamba ga gwamnatin Isra'ila domin kawo karshen bala'in jinƙai.

“Za mu yi aiki don kara matsin lamba ga gwamnatin Isra'ila a cikin kwanaki masu zuwa don hana bala'in jinƙai a Gaza,” in ji shi, yana mai jaddada cewa Turkiyya tana samun cikakken haɗin kai da abokan hulɗarta na duniya.

Yayin da yake sake tabbatar da goyon bayan Turkiyya ga Falasɗinawa, ya kara da cewa: “Za mu tabbatar da cewa 'yan'uwanmu a Gaza sun ji ƙarfin cewa ba su kadai ba ne. Za mu ci gaba da aiki don samun tsagaita wuta a yankin da kuma cim ma zaman lafiya mai ɗorewa.”

Erdogan ya kuma yi maraba da alamun ƙaruwar goyon baya ga kafa ƙasar Falasɗinu a Turai, yana mai cewa Turkiyya tana kallon irin waɗannan matakan a matsayin “masu daraja da ƙarfafa gwiwa.”

“Muna matuƙar daraja kukan da al’umma ke yi da ke tasowa daga Turai. Muna maraba da kowane mataki da aka ɗauka don amincewa da ƙasar Falasɗinu,” in ji shi.

Maganganunsa sun zo ne a yayin da Gaza ke fuskantar ɗaya daga cikin mafi munin rikice-rikicen jinƙai a tarihin baya-bayan nan, inda sama da Falasɗinawa 60,000 suka rasa rayukansu tun daga ranar 7 ga Oktoban 2023, tare da tsananin ƙarancin abinci, ruwa, da kayan magani.

Kiran duniya don tsagaita wuta da ɗaukar matakin hukuma ya ƙara ƙarfi, tare da shari'o'i na doka da ake gudanarwa kan Isra'ila a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya da Kotun Shari'a ta Duniya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#