Dollar

38,7102

-0.18 %

Euro

43,4554

0.14 %

Gram Gold

4.010,2600

1.24 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Katsewar lantarki ta dakatar da ayyuka, da ta’azzara wahalhalun da mutane ke sha, in ji hukumar lantarki ta kasar.

Mayakan RSF sun kai harin da ya katse lantarki a Khartoum

A yammacin Laraba hukumar samar da lantarki ta Sudan ta ce mayakan RSF sun kai hari kan tashoshin lantarki biyu da jirgi marar matuki inda suka janyo katsewar lantarki a babban birnin Khartoum.

“Jirgin yaki marar matuki na ‘yan tawayen ya kai hari kan tashar lantarki ta Al-Markhit da wata tashar rarraba lantarki a garin Omdurman,” in ji hukumar a wata sanarwa.

Ta ce harin “ya janyo katsewar lantarki a Khartoum, wanda hakan ke kara ta’azzara wahalar da ‘yan kasa ke sha da katse ayyuka.”

“Ma’aikatan kashe gobara na ta kokarin kashe wutar da ta kama. Daga baya za a yi nazari kan asarar da hare-haren suka janyo, sannan a dauki matakan gyara,” in ji sanarwar.

Yakin neman kwace iko

Tun watan Afrilun 2023, RSF ke yaki da sojojin Sudan a kokarin kwace iko da kasar, wanda ya janyo asarar dubunnan rayuka da janyo daya daga cikin mafiya munin rikicin jin kai a duniya.

Fiye da mutum 20,000 ne suka rasa rayukansu yayin da wasu miliyan 15 suka rasa matsugunansu, in ji MDD da mahukuntan yankin. Sai dai kuma binciken da kwararru daga Amurka suka yi ya ce adadin adanda suka mutu ya kai mutum 130,000.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#