Dollar

38,7470

-0.11 %

Euro

43,5728

0.26 %

Gram Gold

3.998,9000

-1.35 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

A bana dai maniyyata 15,891 ne daga Nijar za su yi aikin Hajji

Hajjin 2025: Jirgin farko dauke da alhazai 363 'yan Nijar ya tashi zuwa Saudiyya

Jirgin farko ɗauke da mahajjata 363 ‘yan Nijar ya tashi daga filin jirgin sama na Diori Hamani na babban birnin kasar Yamai a ranar Talata 13 ga watan Mayun 2025 zuwa brinin Madina na kasar Saudiyya.

A hukumance dai jirgin ya tashi ne a gaban jakadan Saudiyya a Nijar, Zaid Al Harbi da Daraktan ofishin Firaiministan kasar, Ousman Samba da kwamishinan hukumar aikin Hajji da Umrah (COHO) mai barin gado Sheikh Ali Ben Sallah, da kuma wasu shugabannin kamfanonin sufuri.

Tun da farko dai hukumar COHO ta shirya tashin alhazan ne a ranar Alhamis 8 ga watan Mayun da ya gabata, amma sai aka samu tsaiko, lamarin da kwamishinan hukumar ya tabbatar wa alhazan cewa an yi kokarin shawo kan duk wata matsala da za ta iya shafa su ne shi yasa aka daga tafiyar kana ya yaba wa musu bisa hakuri da kuma juriya.

Sheikh Ali Ben Salah ya kuma bukace alhazan da su wakilci Nijar cikin mutunci tare da yi mwa kasar addu’a.

Kamfanin Niger Airlens tare da hadin gwiwar Flyadeal ne suka samu damar jigilar alhazai ta jiragen haya a bana.

A bana dai maniyyata 15,891 ne daga Nijar za su yi aikin Hajji.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#