Kasancewarta a Yammacin Afirka da kan iyakoki da Benin da Nijar da Chadi da Kamaru, ya sa Nijeriya tana da wani muhimmin wuri na cinikayya da kuma kaikomo tsakanin Yammacin da Tsakiyar Afirka.

Masu safarar miyagun ƙwayoyi suna neman mayar da Nijeriya wurin ya da zango – NDLEA

Hukumar NDLEA mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Nijeriya ta yi zargin cewa ana samun ƙaruwar ‘yan ƙasashen waje masu hannu a safarar miyagun ƙwayoyi ta hanyar Nijeriya zuwa wasu sassan duniya.

Hukumar ta bayyana cewa an kama ‘yan Afirka ta Kudu uku bisa hannu a safarar heroin da koken da tabar wiwi mai yawa.

Mataimakin Darakta a ɓangaren watsa labarai da ba da shawarwari na NDLEA, Francis Okogun, ne ya bayyana wannan ranar Alhamis a lokacin zantawa na haɗin gwiwa da manema labarai da hukumomin tsaro da na tattara bayanan sirri suka yi a Abuja.

Ya yi zargim cewa wasu ‘yan ƙasashen ƙetare suna ƙoƙarin wucewa da miyagun ƙwayoyi ta Nijeriya ta haramtacciyar hanya a madadin ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙayoyi na ƙetare, yayin da wasu ke ƙoƙarin kawo ƙayoyi cikin ƙasar.

Kasancewarta a Yammacin Afirka da kan iyakoki da Benin da Nijar da Chadi da Kamaru, ya sa Nijeriya tana da wani muhimmin wuri na cinikayya da kuma kaikomo tsakanin Yammacin da Tsakiyar Afirka.

Okogun ya ce hukumar tana bincike a kan kamen domin tabbatar da inda aka yi niyyar kai ƙwayoyin da kuma gano ƙungiyoyin da ke da hannu a safarar ƙwayoyin.

“A cikin lokacin da aka yi nazari a kai, an kama mutum uku. Abin da ya sa wannan kamen yake da muhimmanci shi ne ƙwayoyi masu yawa da aka samu a wajen su, ciki har da heroin da koken da tabar wiwi da aka sarrafa wanda aka fi sani da suna Loud.”

Ɗaya daga cikin waɗanda aka kama ɗin ita ce wata ‘yar Afirka ta Kudu mai suna, Gebashe Sithandiwe Jessie, wadda aka kama a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Port Harcourt a watan Oktoban 2026 bisa zargin ƙoƙarin safarar tabar wiwi da aka sarrafa wanda aka fi sani da suna Thai Loud da ya kai kilogiram 32.74 a ɓoye a cikin kayayyakinta.

Wata ‘yar ƙasar Afirka ta Kudu ɗin kuwa Will Jessica Ann, mai shekara 38, an kama ta ne a filin jiragen sama na ƙasa da ƙasa na tunawa da Nnamdi Azikiwe, da ke Abuja, ranar 6 ga watan Yulin 2026, da bulo 14 na heroin da nauyinsu ya kai kilogiram 5.75.

Okogun ya ce kamen na da muhimmanci domin yawan miyagun ƙwayoyin da aka ƙwace da kuma alaƙar da ake ganin suna da shi da ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙasa da ƙasa.

Ya ƙara da cewa hukumar tana gudanar da cikakken bincike domin gano ƙungiyoyin da ke da hannu a safarar miyagun ƙwayoyin.

TRT Afrika — TRT Afrika

#