Dollar

40,6786

0.07 %

Euro

47,1468

-0.04 %

Gram Gold

4.403,7300

0.19 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Yara fiye da 640,000 na fuskantar barazanar tashin hankali da yunwa da kwalara a Arewacin Darfur, kamar yadda hukumar MDD ta bayyana a gargaɗinta

Kwalara ta kashe mutum 80, mutum 2,100 sun kamu da ita a yankin Darfur na Sudan

Aƙalla mutum 80 sun mutum kuma an samu mutane fiye da 2,100 ɗauke da cutar kwalara a jihohi biyar da ke yankin Darfur na Sudan zuwa ranar 30 ga watan Juni, in ji Asusun Kula Da Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNICEF) ranar Lahadi.

A wata sanarwa, UNICEF ya ce cutar ta yi sanadin mutuwar mutum 20 yayin da aka samu mutum 1,180 da suka kamu da cutar a Tawila, a Jihar North Darfur tun ranar 21 ga watan Yuni.

“A fadin jihohi biyar na Darfur, jumullar waɗanda suka kamu da cutar kwalara zuwa ranar 30 ga watan Juli ya kusa kaiwa 2,140, inda aƙalla 80 suka rasa rayukansu,” in ji sanarwar.

Hukumar ta MDD ta yi gargaɗin cewa yara fiye da 640,000 suna fuskantar barazanar tashin hankali da yunwa da cutar kwalara a faɗin Arewacin Darfur.

“Duk da cewa cuta ce da ake iya kaucewa kamuwa da ita a kuma magance ta cikin sauƙi, kwalara tana yaɗuwa cikin Tawila da ma sauran wurare a Darfur, lamarin da ke barazana ga rayukan yara, musamman mafi ƙanƙanta da kuma mafi rauni,” in ji Sheldon Yett, wakilin asusun UNICEF a Sudan.

Duk da matakan da ake ɗauka wajen daƙile yaɗuwar cutar, “yaƙi babu ƙaƙƙautawa yana ƙara buƙatu sama da yadda za mu iya ba da agaji,” in ji Yett.

Ya yi kira da a samar da “damar shige da fice cikin tsaro babu matsi cikin gaggawa domin a sauya halin da ake ciki da taimaka wa yara mabuƙata.”

“Ba za su iya sake jira ko na kwana ɗaya ba.”

Alƙaluman MDD sun nuna cewa fiye da mutum 94,170 sun kamu da cutar kwalara, kuma an ba da rahoton mutuwar fiye da mutum 2,370 a 17 daga jihohi 18 na Sudan daga watan Agustan shekarar 2024.

Sudan na fama da yaƙi tsakanin sojin ƙasar da rundunar RSF tun watan Afrilun shekarar 2023, inda aka kashe mutum fiye da 20,000 kuma aka raba mutum miliyan 14 da gidajensu, in ji MDD da hukumomin cikin ƙasar. Sai dai kuma bincike daga jami’o’in Amurka sun kiyatsa cewa adadin waɗanda suka mutu zuwa yanzu ya kai mutum 130,000.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#