Sport
Dollar
40,6794
0.07 %Euro
47,1555
-0.02 %Gram Gold
4.414,4800
0.43 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Tallafin, wanda ya haɗa da kayayyakin da aka sarrafa da koko da wanda aka samar a Ghana, an miƙa su ga jakadan Falasdinu a Ghana, Abdul Fattah Ahmed Khalil al-Sattari, wanda ya bayyana godiya mai yawa.
Shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, ya gabatar da tallafin jinƙai mai nauyin ton 40 don isarwa ga al’ummar Falasɗinu, inda yaƙin kisan ƙare-dangi da Isra’ila ke ci gaba da yi ya hallaka fiye da Falasɗinawa 60,000 a Gaza tare da yunwa mai tsanani.
Tallafin, wanda ya haɗa da kayayyakin da aka sarrafa da koko da wanda aka samar a Ghana, an miƙa su ga jakadan Falasdinu a Ghana, Abdul Fattah Ahmed Khalil al-Sattari, wanda ya bayyana godiya mai yawa.
‘‘Muna godiya da wannan tallafi. Dukkanmu mun san cewa a Gaza yanzu akwai yunwa da kisan ƙare-dangi,’’ in ji al-Sattari.
A jawabin da ya yi a taron da aka gudanar a Accra a ranar Juma’a, Shugaba Mahama ya yi Allah wadai da kashe-kashen da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma korar Falasdinawa daga gidajensu.
Ghana na goyon bayan two-state solution
''Wannan (tallafin abinci) yana da ma’ana biyu, na alama da kuma na aiki. Na alama saboda koko yana daga cikin kayayyakin da Ghana take alfahari da su. Na aiki saboda koko abinci ne mai matuƙar amfani ga lafiya,'' in ji shugaban na Ghana kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ruwaito.
''Muna fatan cewa waɗannan kayayyakin na koko za su kawo natsuwa da gina jiki da kuma nuna goyon bayanmu ga iyalan da ke fuskantar wahala mai tsanani,’’ in ji Shugaba Mahama.
''Yana da muhimmanci a matsayinmu na al’umma ta duniya mu kare rayuka, mu kare mutunci, kuma mu tsaya tsayin daka wajen tabbatar da adalci da zaman lafiya,'' kamar yadda ya ƙara da cewa.
''Saboda haka, muna kira ga al’ummar duniya da kada su yi ƙasa a guiwa wajen tallafa wa duk wani yunƙuri na samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin tare da bayar da muhimmin tallafin jinƙai ga waɗanda abin ya shafa.''

Shugaba Mahama ya sake jaddada goyon bayan ƙasarsa ga mafitar two-state solution wato samar da ƙasashe biyu kowace mai cin gashin kanta.
''Muna nan daram wajen goyon bayanmu ga tattaunawar da za ta kai ga mafitar two-state solution. Wannan ya yi daidai da dokar duniya da kuma ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya,'' in ji Shugaban Ghana.
Comments
No comments Yet
Comment