Sport
Dollar
40,6793
0.07 %Euro
47,1559
-0.02 %Gram Gold
4.417,8400
0.51 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Gidajen burodi da sauran masu sarrafa fulawa a Nijar za su tafi yajin aikin ne sakamakon wata sabuwar doka wadda ta tilasta musu amfani da fulawa nau’in T55 da T65 da ba a iya samu a ƙasar cikin sauƙi
Ƙungiyar Ma’aikatan Gidajen Burodi da Masu Sarrafa Fulawa ta Jamhuriyar Nijar (SPBPN) ta sanar da shiga yajin aiki na ƙasa baki ɗaya na tsawon sa’o’i 48.
Ƙungiyar ta ce za ta fara yajin aikin ne daga ranar Litinin 4 ga Agusta zuwa Talata 5 ga Agustan 2025.
Wannan na zuwa ne a matsayin martani ga wata sabuwar doka daga gwamnatin ƙasar wadda ƙungiyar ke ganin ba za a iya aiwatar da ita ba kuma tana barazana ga rayuwar masana'antar burodi da tuni take fama da matsaloli.
Ƙungiyar ta nuna damuwarta kan tilasta amfani da fulawa nau’in T55 da T65 da ba a iya samu a ƙasar cikin sauƙi, tare da tsokaci kan cewa kusan kashi 98 na fulawa ana shigowa da ita ne daga ƙasar Aljeriya cikin mawuyacin yanayi.
Lamarin ya ƙara hargitsewa ne bayan rahoton hukumar kula da ingancin kayayyaki ta ƙsar ANMC wanda ya zargi dukkan gidajen burodin Nijar da saɓa ƙa’idoji, abin da ƙungiyar masu gidajen burodin ta ƙaryata.
SPBPN ta jaddada cewa farashin burodi a Nijar shi ne mafi araha a yammacin Afirka duk da tsadar kayan masarufi, kuma wannan yana faruwa ne sakamakon sadaukarwar 'yan masana’antar.
Sun roki gwamnati ta gaggauta duba dokar, inda suka ce barin dokar ta ci gaba da aiki zai janyo rufe gidajen burodi da rasa ayyuka da kuma ƙuntata wa jama'a.
Duk da za ta tafi yajin aiki, ƙungiyar ta ce ƙofarta a buɗe take domin tattaunawa.
Comments
No comments Yet
Comment