Hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kaiwa ta sama da ta kasa a Gaza — wadanda suka shiga kwana na 41 — sun yi sanadin mutuwar Falasadinawa 11,500, ciki har da kananan yara 4,710 da mata 3,160, a cewar hukumomin Falasdinu.

KAI-TSAYE: Isra'ila ta ki amincewa da kudurin MDD na tsagaita wuta a Gaza

Alhamis, 16 ga watan Nuwamba, 2023

0620 GMT — Isra'ila ta ki amincewa da kudurin MDD na tsagaita wuta

Ma'aikatar Harkokin Wajen Isra'ila ta yi watsi da kudurin da Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya wanda ya amince a "tsagaita wuta" a Gaza.

A wata sanarwa da jaridar Haaretz ta wallafa, ta ambato ma'aikatar tana cewa "babu wata kafa ta tsagaita bude wuta" muddin kungiyar Hamas ta Falasdinawa ta ci gaba da rike mutanen da ta yi garkuwa da su.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ranar Laraba ya amince da wani daftari wanda ya yi kira a "gaggauta tsagaita wuta" a fadin Gaza.

Kasashe goma sha biyu ne suka amince da kudurin wanda kasar Malta ta gabatar, yayin da Amurka da Birtaniya da Rasha suka kaurace wa kada kuri'a.

0400 GMT — An kashe wasu sojojin Isra'ila a Gaza

An kashe karin sojojin Isra'ila biyu a gumurzun da ake yi a Zirin Gaza, a cewar kafar watsa labarai ta gwamnatin Isra'ila KAN.

Kafar watsa labaran ta ambato wasu majiyoyi sojin kasar suna cewa an kuma jikkata wasu sojojin kasar biyu a fafatawar.

Hakan na nufin an kashe sojojin Isra'ila hamsin da daya tun 27 ga watan Oktoba.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da fuskanta kalubale s yayin da suke kutsawa Gaza/ Hoto: Reuters

0342 GMT — 'Yan Majalisar Dokoki 24 na jam'iyyar Democrat sun bukaci shugaban Amurka ya sa a tsagaita wuta a Gaza

'Yan majalisar wakilai ashirin da hudu na jam'iyyar Democrat ranar Laraba sun bayyana "matukar damuwa" game da hare-haren da Isra'ila take kaiwa a Gaza, sannan suka yi kira ga shugaban Amurka Joe Biden ya sa a tsagaita wuta.

A wasikar da suka aika wa Biden, 'yan majalisar, wadada suka hada da Alexandria Ocasio-Cortez da Betty McCollum, sun ce an "yi mummunar keta doka" kan kananan yara a Gaza.

Sun kara da cewa dole a tsagaita wuta idan ba haka ba Isra'ila za ta ci gaba da kashe fararen-hula kuma hakan zai jefa Amurka cikin yaki "mummuna kuma mara hikima" da za a yi a fadin Gabas ta Tsakiya.

Alkaluman baya bayan nan sun nuna cewa Isra'ila ta kashe Falasdinawa 11,500, ciki har da kananan yara 4,710 da mata 3,160, a cewar hukumomin Falasdinu.

0142 GMT — Samar da kasashe biyu ita ce mafita ga rikicin Isra'ila da Falasdinawa, in ji Biden

Rundunar sojin Isra'ila ta bai wa mutanen Khan Yunis wa'adin fita daga yankin zuwa kudancin Gaza. / Hoto: Reuters

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ya bayyana wa Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa samar da kasashe biyu ita ce mafita kadai game da rikicin Isra'ila da Falasdinawa kuma sake mamaye Gaza zai kasance babban kuskure.

Biden ya shaida wa manema labarai cewa yana daukar dukkan matakan da suka dace bisa karfin ikon da yake da shi domin ganin an kubutar da mutanen da kungiyar Hamas ta yi garkuwa da su, sai dai ya ce ba ya nufin daukar matakin soji.

"Ba na so na yi gaban kaina a wannan lamari domin ban san abin da ya faru ba a awanni hudu da suka gabata, sai dai mun samu babban hadin kai daga kasar Qatar," in ji shi a yayin da aka tambaye shi game da ci-gaban da ake samu kan mutanen da aka yi garkuwa da su ranar 7 ga watan Oktoba.

#