Yaƙin da Isra'ila take yi a Gaza — wanda ya shiga kwana na 421 a yau — ya kashe Falasɗinawa fiye da 44,363 da jikkata fiye da mutum 105,070. A Lebanon kuwa, Isra'ila ta cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta bayan kashe mutum 3,961 tun daga Oktoban bara.

Kai-tsaye: Isra'ila ta kai hari Gaza a daidai lokacin da wakilan Hamas suka tafi Masar tattaunawar tsagaita wuta

0500 GMT — Wakilan Hamas sun nufi birnin Alkahira na Masar domin tattaunawa kan yiwuwar tsagaita wuta a Gaza, kamar yadda wani jami'i na ƙungiyar ta Hamas ya bayyana.

Sai dai duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta tayar da bam a unguwar Sheikh Radwan da ke cikin birnin Gaza inda ta kashe Falasɗinawa 10.

Wani jirgin yaƙin Isra'ila ya kai hari kan wani gida mallakar iyalan as-Sardi da ke unguwar inda farar hula 10 suka rasu, wasu kuma suka jikkata, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Isra'ila WAFA ya tabbatar.

0030 GMT — An gudanar da zanga-zanga 105 a biranen Morocco 48 domin nuna goyon baya ga Gaza

An gudanar da zanga-zanga 105 a ranar Juma'a a biranen Moroko 48 don yin tir da hare-haren Isra'ila da nuna goyon baya ga Gaza.

Dubban jama'a ne suka taru a wuraren da jama'a ke yin zanga-zangar domin amsa kiraye-kirayen kungiyoyin fararen hula, ciki har da hukumar kare muradun al'ummar kasar Morocco.

Masu zanga-zangar sun nuna bacin rai da nuna goyon baya ga al'ummar Falasdinu

#