Rahotanni sun bayyana Alice Huang a matsayin matar da ake zargi da yi wa China leƙen asiri kuma tana da kusanci da Jensen Huang, shugaban kamfanin Nvidia. Sannan tsohon kamfanin da ta yi aiki na fuskantar bincike kan zargin aika fasahar AI zuwa China

Wace ce Alice Huang, matar da ake zargi da yi wa China leƙen asiri?

Ana zargin wata babbar jami'ar fasaha mai suna Alice Huang da yi wa China leƙen asiri ta hanyar wata alaƙar soyayya da shugaban kamfanin Nvidia, Jensen Huang, kamar yadda wasu kafafen yaɗa labarai suka ruwaito.

Matar wadda ake kuma kiranta da Huang Le, ta taɓa riƙe wani babban muƙami a kamfanin adana bayanai (data centres) na Megaspeed International, mai hedikwata a Singapore. Sai dai bayanai kan asalinta ba su da yawa.

Wace ce Alice Huang?

Jaridar The New York Times, wadda ta fara wallafa rahoton zargin wani shirin leƙen asiri, ta ce jami'an Amurka na zargin cewa Beijing ta ɗauke Alice aiki ne don tattara bayanan sirri game da shugaban kamfanin Nvidia.

Duk da cewa sunan babbansu iri ɗaya ne da Jensen Huang, amma ba ‘yan uwa ba ne. Jensen Huang mai shekara 63, haifaffen dan kasar Taiwan ne, kuma shi ne shugaban kamfanin Nvidia na Amurka da ke kera na’urar chip na kwamfuta da ke amfani da fasahar basirar ɗan'adam (AI).

Jaridar The Times, wadda ta dogara da bayanan mutanen da aka yi wa bayani kan binciken da aka gudanar, ta bayyana Alice Huang a matsayin wadda ta iya Turanci sosai kuma take da kusanci da manyan jami'ai a masana'antar na’urar chips ta fasahar AI a duniya.

Binciken da aka gudanar a intanet ya kuma gano wani shafi mai ɗauke da hotonta a wata rumbun bayanan asusun zuba jari ta China, inda aka wallafa cewa ta taɓa aiki a bankin HSBC da kuma aikin a matsayin 'yar jarida a kafafen watsa labaran China na CCTV da Hunan TV.

Sai dai kamfanin dillancin labarai na AFP bai iya tabbatar da sahihancin wannan bayanin ko wanda ya wallafa shi ba.

Wace alaƙa ce ke tsakanin su?

Rahotannin kafafen yaɗa labarai a makon da ya wuce sun bayyana cewa mutanen biyu suna da kusanci.

A ranar Lahadi, Jensen Huang ya shaida wa ma'aikatan Nvidia cewa yana matuƙar baƙin ciki, tare da neman afuwa kan ‘‘cin amana ,matarsa da ya yi’’.

Hotuna da bidiyon kai-tsaye daga wasu tarukan masana'antu a shekarun 2024 da 2025 sun nuna mutane biyun tare.

Wane ne kamfanin Megaspeed?

A cewar jaridar The New York Times da The Wall Street Journal, jami'an Amurka sun kammala bincikensu a shekarar bara cewa Alice Huang na ƙoƙarin kusantar Jensen Huang domin yi masa leƙen asiri.

A lokacin, rahotanni sun bayyana cewa tana riƙe da babban muƙami a kamfanin Megaspeed International, wanda ke ba kamfanoni damar hayar ƙarfin sarrafa kwamfuta domin horar da tsarin AI da kuma gudanar da ayyukansu.

Megaspeed ya bayyana kansa a matsayin "babban abokin hulɗar kasuwancin Nvidia a fannin samar da ƙarfin sarrafa rumbun adana bayanai na kwamfuta a yankin Asiya da Pacific".

Shafin kamfanin na LinkedIn ya nuna cewa yana da ofisoshi a Singapore, da Malaysia da kuma Indonesia.

Bayanan hukumomin gwamnatin Singapore sun nuna cewa a baya ana kiran kamfanin da suna 7Road International, lamarin da ke nuna alaƙarsa da kamfanin kera kwamfuta na wasanni na China mai suna 7Road.

Shin Megaspeed ya taimaka wa China kauce wa takunkumin Amurka kan fasahar Chip na kwamfuta?

Amurka ta sanya takunkumin hana fitar da wasu daga cikin manyan fasahar Chips na Nvidia zuwa China, bisa dalilan da suka shafi tsaron ƙasa.

Jaridar The New York Times ta ruwaito cewa tun shekarar 2024 Washington ke gudanar da bincike kan Megaspeed bisa zargin ƙoƙarin karkatar da fasahar chip na kamfanin Nvidia zuwa China.

Rahotanni sun kuma ce hukumomin Singapore sun gudanar da bincike kan kamfanin tare da yi wa Alice Huang tambayoyi a shekarar 2025.

A bara, kamfanin dillancin labarai na Bloomberg ya ruwaito cewa hukumomin Singapore sun gudanar da bincike kan zargin safarar fasahar Chips ba bisa ƙa'ida ba.

A watan Disamban 2025, Megaspeed ya ƙaryata rahoton Bloomberg, yana mai cewa rahoton "ya ƙunshi bayanai masu ruɗani da zarge-zarge marasa inganci, ciki har da ikirarin cewa ‘‘kamfanin na da hannu cikin safarar fasahar Chip na Kwamfuta ba bisa ƙa'ida ba".

A cewar AFP, wata lambar wayar da aka wallafa a shafin yanar gizo na Megaspeed na hade da layin waya na wani gida, kuma Mutumin da ya amsa wayar ya ce bai san komai game da kamfanin ba.

AFP ta kuma tuntubi rundunar 'yansandan Singapore da ma'aikatar harkokin cikin gida domin jin ta bakinsu, amma ba ta samu amsa ba kafin wallafa rahotonta.

TRT Afrika — TRT Afrika

#