Dollar

40,6648

0 %

Euro

47,1022

-0.18 %

Gram Gold

4.410,0100

0.33 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Da aka tambayi Iran a kan ko za ta shiga tattaunawa kai-tsaye da Amurka, sai Tehran ta ce "A'a."

Iran ta ja kunne cewa Amurka za ta ɗauki alhakin hare-haren cibiyoyin nukiliya a tattaunawa ta gaba

Iran ta bayyana cewa za ta ɗora alhakin hare-haren da aka kai wa wuraren nukiliyarta a kan Amurka a duk wata tattaunawa ta gaba da za a yi, tare da ƙin amincewa da yin magana kai-tsaye da Washington.

Amurka ta kai hari kan muhimman wuraren nukiliyar Iran a ranar 22 ga Yuni, inda ta shiga cikin wani yaƙi da Isra'ila ta fara wanda ya katse tattaunawar da ake yi kan shirye-shiryen nukiliyar Tehran.

“A cikin kowace tattaunawa da ake sa ran cim ma daidaito... batun ɗora alhakin hare-haren soja da kuma neman diyya kan Amurka saboda kai hari kan wuraren nukiliyar Iran, zai kasance ɗaya daga cikin batutuwan da za a tattauna,” in ji mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran, Esmaeil Baqaei, a wani taron manema labarai a ranar Litinin.

Da aka tambaye shi ko Iran za ta shiga tattaunawa kai-tsaye da Amurka, Baqaei ya ce: “A’a.”

A tsakiyar watan Yuni, Isra'ila ta ƙaddamar da wani hari mai tsanani kan wuraren nukiliya da sojojin Iran, har ma da kai hari kan wuraren zama na fararen hula a cikin kwanaki 12 na yaƙi, wanda sojojin Amurka suka shiga ta hanyar kai hari kan wuraren nukiliya a Fordow, Isfahan da Natanz.

Yaƙin ya katse tattaunawar da aka fara a watan Afrilu, wacce ita ce mafi girma tsakanin Tehran da Washington tun bayan da Amurka ta janye daga yarjejeniyar nukiliya ta tarihi a shekarar 2018.

Bayan yaƙin, Tehran ta dakatar da haɗin kai da hukumar kula da nukiliya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (IAEA) kuma ta nemi tabbacin cewa ba za a sake kai mata hari ba kafin ta koma kan teburin tattaunawa.

Washington ta yi watsi da kiran Tehran na neman diyya, tana mai cewa wannan abu ne “mai ban dariya.”

Baqaei ya ce a ranar Litinin cewa Iran tana bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, amma ya soki abin da ya kira “matsayin siyasa da rashin ƙwarewa” na hukumar IAEA.

Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Wajen ya ce Mataimakin Shugaban IAEA ana sa ran zai ziyarci Iran “cikin ƙasa da kwanaki 10.”

A watan da ya gabata, Iran ta ce haɗin kai na gaba da hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya zai ɗauki “sabon tsari.”

A ranar 25 ga Yuli, jakadun Iran sun gana da takwarorinsu daga Jamus, Birtaniya da Faransa, a karo na farko tun bayan kawo ƙarshen yaƙin da Isra'ila.

Ƙasashen Turai uku suna cikin yarjejeniyar nukiliya ta 2015, wacce ta rushe bayan Amurka ta janye a lokacin wa’adin farko na Trump.

A makonnin da suka gabata, ƙasashen uku sun yi barazanar sanya takunkumi idan Tehran ta kasa amincewa da yarjejeniya kan haƙar uranium da haɗin kai da masu binciken Majalisar Ɗinkin Duniya.

Iran ta maimaita cewa sake sanya takunkumi “ba sa kan doka ba” kuma ta nace kan haƙƙinta na haƙar uranium.

Isra'ila da Ƙasashen Yamma suna zargin Iran da neman ƙera makaman nukiliya, zargin da Tehran ta sha musantawa.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#