Dollar

40,6594

-0.01 %

Euro

47,1021

-0.19 %

Gram Gold

4.407,6700

0.28 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Wani sabon bincike da aka wallafa a The Lancet ya nuna cewa gurɓata muhalli da ake yi saboda zubar da sharar robobi na jawo asarar fiye da dala tiriliyan 1.5 duk shekara wajen magance cututtukan da hakan ke jawowa.

Duniya tana asarar dala tiriliyan 1.5 a fannin lafiya sakamakon gurɓata muhalli da bolar robobi

Gurbacewar muhalli daga sharar robobi na jawo asarar fiye da dala tiriliyan 1.5 a fannin tattalin arzikin lafiya da ke da nasaba da lafiyar jama’a a kowace shekara, kuma yana jawo cututtuka da mace-mace a kowane mataki na rayuwa, a cewar wani sabon rahoto da aka wallafa a ranar Lahadi a Mujallar Lafiya ta The Lancet.

Mawallafan rahoton sun rubuta cewa “duniya na cikin bala’in bolar robobi. Amma abu ne da za a iya magancewa.”

Sun nemi a samar da matakai na kimiyya da dokoki ciki har da na cin tarar kuɗaɗe, irin waɗanda aka yi amfani da su wajen daƙile gurɓata iska da gubar dalma.

Bayanai sabon binciken ne zuwa ne a lokacin da tawagar da Majalisar Dinkin Duniya ke jagoranta don samo mafita ke shirin yin zamanta na gaba a Geneva, inda za ta dauki matakin ƙarshe kan matsalar bolar robobi da ta gallabi duniya.

Binciken ya yi gargadin cewa matsalar bolar robobi na ta’azzara, inda take yin mummunar illa ga bil adama da ma duniya baki ɗaya.

A cewar binciken, samar da robobi ya ƙaru daga ton miliyan biyu a 1950 zuwa tom miliyan 475 a 2022, kuma ana sa ran zai ƙaru zuwa ton biliyan 1.2 nan da shekarar 2060.

An fitar da sakamakon binciken ne a yayin da ake shirin komawa teburin tattaunawa kan makomar bolar robobi a duniya a mako mai zuwa a Geneva.

Daga ranar 5 zuwa 14 ga watan Agusta, wakilai daga kasashe fiye da 170 za su yi kokarin farfado da wata yarjejeniya ta doka ta dakile gurbatar muhalli da robobi.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#